‘Yan sandan jihar Barno sun garkame hedikwatar jam’iyyar NNPP dake garin Maiduguri jihar Barno ranar Alhamis.
Shugaban jam’iyyar na jihar Barno Muhammed Mustapha ya ce sun waye gari ranar Alhamis suka iske ofishin jam’iyyar garkame da manyan kwado sannan kuma sojoji sun girke mototin yaki a gaban ofishin jam’iyyar.
” Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rabiu Kwankwaso zai ziyarci garin Maiduguri domin kaddamar da ofishin sannan kuma ya gana da ‘yan jam’iyyar.
Amma kuma da muka garzaya ofishin ‘yan sanda domin samun karin bayani sai aka sanar da mu cewa wai gwamnati ne ta ce a garkame ofishin saboda wai mun kama hayan ofis ne a rukunin gidaden zama da ba a halatta bude ofis a wurin ba.
Mustapha ya kara da cewa ” Wannan maganar banza ce domin ko a doka an ce idan mutum ya bude ofis irin haka a rukunin gidaje akan bashi notis ne sannan kuma a bashi wa’adin wata shida ya kama wani wurin.
Sannan da muka tuntubi shugaban ‘yan sanda na jihar Abdu Umar, domin karin bayani ya ce mana jami’an su sun zo wannan wuri ne domin su samar da tsaro, rikici ne tsakanin jam’iyyar da gwamnatin jiha, babu ruwan su.
Shugaban jam’iyyar na kasa Rufai Alkali, ya ce abin yayi matukar ba su mamaki, a ce an wayi gari kwatsam sai yan sanda su garkame mana ofis sannan su kama dan takarar sanata na jam’iyyar, ” Tsakani da Allah a ina ake irin wannan zalincin?
Discussion about this post