Wani rahoton da Bankin Duniya ya fitar a cikin 2021 ya tabbatar da cewa akwai mutanen da ba su amfani asusun ajiya a bankuna har mutum biliyan 1.4 a duniya.
Rabin mutanen da ba su ajiyar kuɗi a banki a duniya su na Najeriya, Indiya, Masar, Chana, Bangaladish, Indonesiya da Pakistan.
Rahoton ya ci gaba da cewa rabin waɗanda ba su amfani da bankuna a duniya duk su na cikin ƙasashe shida masu tasowa a ɓangaren tattalin arziki, sai kuma Chana.
Rahoton ya ce waɗanda ba su amfani a asusun ajiya a bankuna ko amfani da kafafen zamani wajen hada-hadar kuɗaɗe a waɗannan ƙasashen bakwai za su kai mutum miliyan 740.
Sai dai kuma a lura da cewa adadin marasa amfani da bankunan ya ragu a faɗin duniya, daga mutum biliyan 2.5 a cikin 2011 zuwa biliyan 1.7 a cikin 2017, sai kuma cikin 2021 da hasashen ƙididdiga ya nuna sun kai biliyan 1.4.
A wannan ƙididdiga dai ana amfani da lissafin magidanta ne, ko kuma baligai maza da mata da su ka haura shekaru 18 abin da ya yi sama.
“A China akwai mutum miliyan 130, Indiya mutum miliyan 230, Pakistan miliyan 115, Indonesiya mutum miliyan 100 sai Najeriya mai kusan kashi 45 bisa 100 na ‘yan ƙasar.
A Najeriya an samu ƙaruwar yawan masu ajiya a banki dalilin shirin zaburar da mutanen karkara amfani da tsarin ajiyar kuɗaɗe a bankuna, wanda CBN ya shigo da shi, wato ‘financial inclusion’.
Cikin watan Mayu ne Mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Aishah Ahmad ta bayyana cewa zuwa yanzu an cimma samun kashi 64 bisa 100 na yawan mutanen da aka so su riƙa ajiyar kuɗaɗe a banki.
Ta ce yanzu kuma an maida hankali domin a samu kusan kashi 95 da adadin waɗanda ake so su ƙaru a yawan masu amfani da asusun bankunan.
Discussion about this post