Kungiyar ‘Buhari Media Organisation BMO’ ta bayyana cewa adadin yawan yaran da ba su makarantar boko a Najeriya miliyan 6.9 ne ba miliyan 10.5 ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke watsawa ba.
A wata sanarwa dake dauke da sa hannun shugaban kungiyar Niyi Akinsiju da sakatariyar kungiyar Cassidy Madueke kungiyar ta bayyana cewa alkaluman yawan yaran da basu makarantar boko da mininstan ilimi ya bayyana shine ainihin yawan yaran da basu da ilimin boko a kasar nan.
“A kwanakin baya wasu kungiyoyi sun bayyana wasu alkaluma a matsayin yawan yaran da basu makaranta a kasar nan ba tare da su tabbatar da alkaluman ba daga wajen hukumomin da ya kamata.
“Abin mamakin shine yadda mutane ke amfani da dadaddun alkaluman yawan yaran dake gararamba a titi a matsayin yawan da har yanzu ke gararamba a titi bayan akwai sabbin alkaluman da ministan ilimi Adamu Adamu ya bada a shekarar 2021 a matsayin miliyan 6.9.
“Alkaluman yawan yaran da basu makarantar boko a kasar nan ya ragu a dalilin Shirin BESDA da gwamnatin Buhari bullo da shi.
“Shirin wanda ya fara aiki a shekarar 2018 da Dala miliyan 612 din da babban bankin duniya ta bada a matsayin taimako don rage yaran da basu makaranta a jihohi 17 a kasar nan.
“A cikin shekara daya Shirin BESDA ta saka yara 1,053,422 cikin makarantar boko a jihohi 17.
Wadannan jihohi sun hada da Adamawa- 25,714, Bauchi- 83,39, Borno -62,336, Ebonyi -65,471, Gombe- 52,600, Jigawa -47,416, Kaduna -39,091, Kano- 302434, Katsina- 26,555, Kebbi- 25,556, Niger -73,568, Oyo- 40,007, Rivers- 22,782, Sokoto- 71,000, Taraba- 24,246, Yobe- 72,000 da Zamfara- 19,055.
Discussion about this post