Tsohon sanatan Kaduna Ta tsakiya a majalisar Dattawa, Sanata Shehu Sani ya caccaki gwamnan jihar Kaduna da zargin cewa lallai yana daga cikin na gabagaba wanda suke ruruta wutan rashin tsaro a jihar Kaduna.
A tattaunawa da sanatan yayi da talbijin din Arise ranar Lahadi, ya ce sannan wasikar da El-Rufai ya aika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari game da matsalar tsaro a jihar Kaduna salo ne na ya zame kansa da ga matsalar.
Ya ce Wannan wasika ta nuna cewa lalli gwamna ya gaza domin babu wani abu sabo a ciki. Duk abinda ya fadi a ciki tun shekarun baya aka san da su a jihar, tun a lokacin shi kan sa gwamnan yana ƙaryata mu idan muka faɗi.
” Ba kamar yadda wasu gwamnonin suke taimaka wa hukumomin tsaro a jihohin su ba, El-Rufai kakagida yayi ya ki taimaka musu da kayan aiki, kai da kuma mai ma ya ki. Sannan kuma irin kalaman da ya rika yi su suka daɗa sa ƴan ta’adda suka kwararo jihar suka hana mutane sakat.
” Bari in gaya muku ku sani, kananan hukumomi biyu ne kacal za ka iya zama a Kaduna cikin kwanciyan hankali, Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu. Suma din ta waje-wajen su, ba za ka kwana idon biyu rufe ba.
Gwamnan ya gaza matuka. Babu wani kokari ko himma da yayi wajen yaƙi da ƴan ta’adda wanda za a ce gashi yau abin a yaba ne. Ya kyale mutane kawai hannu rabbana, idan an sace ƴan uwan su sai kowa yayi ta kan sa kawai, su tara kuɗi su fanshe su.
” A lokacin da nake majalisar Dattawa, na rika tashi ina jawo hankalin gwamnati kan wannan matsala amma mutane irin su gwamna El-Rufai suka yi min zagon kasa suna karyata ni da suka na.
Babu wani abu da sabo a cikin wasikar El-Rufai in ba ma tona wa kan sa asori da yayi ba cewa lallai ya gaza, ya kasa, yana neman kawai ya dora wa wani laifi ne ya zame kansa.
” Kaduna yanzu ta zama dandalin da matattarar ƴan bindiga inda suke cin karen su ba babbaka, kuma tuntuni haka ake, tun idan mun faɗi su El-Rufai suna cewa wai karya muke yi.
” Kauyuka da dama a jihar Kaduna na karkashin ikon ƴan bindiga ne, su suke karbar haraji, sune suke samar wa mutanen kauyuka tsaro sannan har kotuna sun kakkafa suna yi shari’a da dai sauransu.
Discussion about this post