Fitaccen ɗan wasan gasar Big Brother, Khalid ya bayyana wa Ebuka cewa soyayyar da yake yi wa Daniella, ba da wasa yake ba
Idan ba a manta Khalid da Daniella sun yi fice sosai a gidan Big Brother saboda soyayyar da ya shiga tsakanin su a wannan gida na Big Brother.
A ranar Lahadi, an cire Khalifa da Illebaye daga wannan gida.
Da ya ke tattauna wa da Ebuka bayan an fidda shi, Khalid ya ce zai cigaba da harkokin sa da neman damar zama jakada a kamfanoni wanda shine dalilin da ya sa ya shiga gasar.
Bayan haka ya ce yana soyayya da Daniella ba da wasa suke yi ba.
Discussion about this post