Dan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi ganawar sirri da gwamnan jihar Ribas Nysome Wike.
Majiya daga hedikwatar jam’iyyar PDP ta ce an yi ganawar ne a gidan Jerry Gana a Abuja.
Kwamitin Amintattun PDP ya kafa wani kwamitin zama domin ganawa da hasalallun cikin jam’iyya.
Wasu daga cikin waɗanda kwamitin zai zauna da su, sun haɗa da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas da kuma wasu manyan jam’iyya masu goyon bayan sa da kuma masu fushi da fushin Wike.
Shugaban Kwamitin Amintattu ko kuma a ce Kwamitin Dattawa, Walid Jibrin, ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba cewa an kafa kwamitin bayan wani dogon zama na sa’o’i biyu da dattawan jam’iyyyar su ka yi.
Ya ce dukkan mambobin kwamitin su na cikin wannan sabon kwamitin da aka kafa, a matsayin masu shiga tsakani domin a sasanta.
“Mun kafa kwamitin ne domin a samu sulhun rashin jituwar da ke tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike, kai da ma duk wani mai wani ƙullaci da ƙulafuci a cikin zuciyar sa a cikin PDP.”
Sai dai kuma Jibrin bai faɗi tsawon lokacin da kwamitin zai ɗauka ya na aikin sasancin ba.
Da aka tambaye shi ko sun tattauna batun neman saukar Shugaban PDP Iyorchia Ayu da su Wike ɗin su ka jajirce cewa sai dai ya sauka? Sai Jibrin ya ce wannan ba wani abin tattaunawa ba ne, kuma ba su tattauna a kan hakan ba.
Kafa wannan kwamiti ya zo ne cikin gaggawa, kwana ɗaya bayan Wike da magoya bayan sa sun yi wata ganawar da su ka yi gagarimin shirin sa ƙarar wando ɗaya da Atiku.
Koda yake sun yi ganawar cikin sirri ne, wasu daha cikin jigajigan PDP sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ganawa ta yi kyau kuma dukkan su biyu zasu hada kai don ganin jam’iyyar ta nasara a zaben 2023.
Discussion about this post