Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa za ta rufe duka gidajen karuwai dake jihar domin kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a fadin jihar.
Babban sakataren ma’aikatar al’amuran mata da raya al’amuma ta jihar Kaltum Rufa’i da ta sanar da haka wa manema labarai a garin Minna ranar Alhamis.
Rufa’i ta ce duk da cewa akwai dokokin da suka hana tada hankalin mutane ta kowace yanayi a jihar amma ma’aikatar za ta gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.
Karuwan garin Minna
Sakamakon binciken da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya gudanar ya nuna cewa karuwan garin Minna kan fara fitowa daga karfe bakwai na yamma zuwa tsakad dare.
Karuwan sun fi tsayawa a shatale-talen City gate, the Eastern by-pass da gidan man ‘Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC)’ wajen neman kwastamomi.
Wasu cikin karuwan da basu so a fadi sunayen su sun ce sukan karbi Naira 1,000 zuwa 10,000 bisa ga irin shagalin da kwastama ke bukata.
Sun ce wasu kwastamomi kan biya daki a otel daga Naira 1,000 zuwa 3,000 idan mutum na bukatar ya huta na gajeren lokaci ne sannan 5,000 zuwa 8,000 idan mutum na so ayi ta bugawa ne har safe.
Wata cikin karuwan ta ce tana karuwanci saboda rashin aikin yi.
“Dole na samu kudaden biyan bukatu na sannan karuwanci ne kadai aikin dake samar mun da abin biyan bukata ta.
Discussion about this post