Ƙungiyar Gamayyar Ma’aikatan Harkokin Fetur da Gas (NUPENG) ta bayyana goyon bayan cewa za ta shiga cikin zanga-zangar da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) za ta yi a kan yajin aikin da malaman jami’o’i ke yi a ƙarƙashin ASUU.
Shugaban NLC Ayuba Wabba, dai tun a ranar 1 Ga Yuli ya ce Ƙungiyar Ƙwadago za ta fito zanga-zanga idan yajin aikin ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.
An dai shafe watanni biyar kwanan malaman jami’o’i na yajin aiki, wanda su ka fara tun a ranar 14 Ga Fabrairu.
Ganin haka ne su ma Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’i manyan su da ƙanana su ka shiga yajin aikin. Hakan ya janyo gaba ɗayan ayyuka a jami’o’i tun daga koyarwa da ayyukan gudanarwa su ka tsaya cak.
A cikin sanarwar da NUPENG ta fitar, ta tofa wa gwamnatin tarayya yawu a fuska, saboda ta kasa magancewa da kuma shawo kan yadda za a daina yajin aikin.
“Saboda haka mu ma’aikatan NUPENG za mu shiga zanga-zanga domin taya NLC nuna wa gwamnati damuwar mu kan mawuyacin halin da jami’o’in Najeriya ke ciki. Za mu shiga wannan zanga-zangar wadda za a yi a dukkan faɗin ƙasar nan.”
Sanarwar na cikin takarar da Shugaban NUPENG Williams Akporeha da Babban Sakataren NUPENG Afolabi Olawale su ka sanya wa hannu.
NUPENG ta ce ta damu ƙwarai da wannan dogon yajin aiki da ASUU, NASU da SSANU ke yi, wanda ya durƙusar da karatun jami’a a faɗin ƙasar nan.
Cikin wannan makon ne ASUU ta maida wa Shugaba Muhammadu Buhari raddi, biyo bayan gargaɗin da ya yi wa ƙungiyar, inda ya ce “yajin aikin ya isa haka nan.
A cikin raddin, ASUU ta ce “yajin aikin bai isa haka nan ba, tukunna ma tukun, tunda gwamnati ta maida darajar jami’o’i kamar darajar sakandare.”
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), ta yi wa Shugaba Muhammadu Buhari raddi kan kurari da roƙon da ya yi masu cewa su koma bakin aiki, saboda “yajin aikin ya isa haka nan.”
ASUU ta bayyana cewa, “ai tukunna ma tukun, yajin aikin bai isa haka nan ba, har sai Shugaban Ƙasa ya tashi ya magance matsalolin da su ka dabaibaye jami’o’i da lalacewar darajar karatun jami’a a ƙasar nan tukunna.”
ASUU ta zargi Buhari da yin watsi da matsalolin dasu ka dabaibaye jami’o’i da su ka haifar da taɓarɓarewar karatun jami’a a Najeriya.
ASUU ta ce Buhari ya na nuna wasu alamomi da sagwangwaman da ba su yi kama da na mai shugabancin ƙasa ba.
A cikin wata sanarwa da Kodinetan ASUU da ke Jihar Legas, Adelaja Odukoya ya fitar kuma ya saka mata hannu a ranar Laraba, ya bayyana cewa, “ai tukunna ma tukun, yajin aikin bai isa ba, tunda aka maida jami’o’i dandalin biyan bukatun ‘yan siyasa da kuma dandalin karkatar da kuɗaɗe da sunan ayyukan mazaɓu.
“Ai yajin aiki tukunna ma tukun, tunda gwamnati ta wulaƙanta darajar jami’o’i, har su ka yi taɓarɓarewar da ake yaje ɗaliban da idan sun fita ba su iyawa kuma ba su da basirar yin aikin da za su ci moriyar kwasa-kwasan da su ka yi, ballantana har su yi gogayya da na wasu ƙasashen duniya.
“Ai yajin aiki tukunna ma tukun, tunda dai gwamnati ta sakwarkwatar da darajar ilmi a jami’o’i, sun koma kusan daraja ɗaya da sakandare.
Discussion about this post