Jam’iyyar APC a jihar Barno ta bayyana kwamishinan shari’a na jihar Barno, Kaka-shehu Lawan wanda zai maye gurbin Shettima a majalisar dattawa.
Idan ba a manta Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu ya zaɓi sanata Kashim Shettima ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a zaɓen 2023.
Bisa wannan dalili, jam’iyyar APC a jihar Barno ta zaɓi Kaka-shehu Lawan ya maye gurbin sanata Shettima a majalisar dattawa.
Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya bayyana cewa zaɓin Shehu daga Allah ne. Ya kara da cewa Kaka-shehu mutumin kirki ne kuma ya bauta wa jam’iyyar APC matuka a jihar Barno.
Daily Nigerian ta buga cewa, Shugaban jam’iyyar APC na jihar Barno Ali Dalori, ya yabawa jam’iyyar da jinjina mata kan zabar Kaka-shehu ya canji Shettima a majalisar.
Discussion about this post