Fadar Shugaban Ƙasa yi raddi ga kamfanin jaridar Daily Trust biyo bayan wani ra’ayin ta da jaridar ta rubuta a ranar Litinin, inda ta yi bayani mai raɗaɗi kan taɓarɓarewar tsaro da tattalin arziki a ƙasar nan.
Garba Shehu, wato Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari, Garba Shehu ya bayyana a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Litinin ɗin, ya ce matsayar da jaridar ta ɗauka molon ka ne kawai.
“Lallai waɗanda su ka buga ra’ayin sun yi gaskiya da su ka ce a duk duniya baki ɗaya ce ana fama da ƙuncin rayuwa.
“Amma kuma a fito a ce wai Gwamnatin Buhari za ta sauka ba tare da ta bar ƙasar nan cikin albarkar da ta fi ta gwamnatin da ta gada ba, musamman a fannin tsaro, tattalin arziki da daƙile rashawa, to wannan iƙirarin molon-ka ne kawai.”
Cikin makonni biyu da su ka gabata ne wannan jarida ta yi binciken bambancin fifiko da sauƙin tsadar rayuwa a lokacin mulkin Buhari da kuma kafin hawan sa cikin 2015.
Binciken wannan jarida ya nuna cewa iƙirarin da Fadar Shugaban Ƙasa ta yi ba gaskiya ba ne.
Tattalin arziki ya ƙara taɓarɓarewa a ƙarƙashin wannan shugaban, yayin da matsalar tsaro da yaƙi da rashawa ma ba za a iya cewa sun an fi samun ci gaba a shekaru bakwai ɗin Buhari kan mulki ba.
Sai dai kuma a ranar Litinin Fadar Shugaban Ƙasa ta sake nanata wannan matsaya cewa mulkin Buhari ya samar da ci gaba sosai fiye da yadda ya samu Najeriya kafin 2015.
Fadar ta ce saɓanin zamanin mulkin Jonathan, a yanzu Boko Haram ba shi riƙe da wani yanki na ƙasar nan, saɓanin kafin Buhari ya karbi mulki.
Shehu ya ce an kakkaɓe ISWAP a yanzu. Sannan kuma ya ce kafin Buhari ya hau mulki, Boko Haram na riƙe da yankin da idan za a auna faɗin sa, ya kai faɗin ƙasar Belgium.
Haka kuma Shehu ya ci gaba da bayyana irin ci gaban da aka samu a fannin tattalin arzikin da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.
Discussion about this post