Fitacciyar mawakiyar Hausa da ta yi fice wajen rera wakokin soyayya a finafinan Hausa Maryam Bakassi, ta bayyana cewa da zarar ta yi aure za ta daina yin waka ko da ko mijin ya amince ta cigaba da yin waka.
Maryam Bakassi ta bayyana haka a hira da ta yi da BBC Hausa, in da ta kara da yin bayani game da inda ta sami suna Bakassi da kuma da kuma takaitaccen tarihinta.
” Na taba zuwa Bakassi ne na ziyarci garin na dawo so sai ‘sister na’ take ce mun ” sannu mutanen Bakassi. Maryam Bakassi kenan!.
To daga lokacin kuma sai na ji mutanen unguwa suna faffadan haka da abokanai na. To inda na samu sunan Maryam Bakassi kenan.
Bakassi ta ce ita ‘ya asalin jihar Gombe ce amma kuma a garin Jos aka haife ta.
” Ni a garin Jos aka haife ni amma asalin iyaye na a garin Gombe suke. Ina da shekara 28. Na yi karatuna gaba daya a Jos ne.
” Na yi ‘primary School’, ‘secondary school’ yanzu ina ‘200 level a university of Jos’.
Bakassi ta bayyana kalubalen da take samu a wajen sana’arta kamar haka” ” Ta fannin sana’o’in da nake ciki ban samu matsaloli da yawa ba kamar ta fannin waka duk wani mawaki, mawakiya Muna zaman mutunci, kowa na karuwa da kowa sai dai dan abin da ba a rasa ba Wanda Kai za ka ga wani na bakin ciki da Kai wannan Kuma ‘Normal’ ne baza kama damu a kai ba.
” To a gaskiya a ta dalilin waka wani abin al’ajibi na tada hankali ko abin tsoratarwa bai taba samuwa da ni ba. Sai dai wani lokaci haka akwai dan matsala da akan dan samu muryana na kama da na mawaka guda biyu.
” Mutane, fans suna ‘Confuse’ akan idan na yi waka ana tunanin wance ce ta yi ita kuma wancan din idan ta yi waka ana tunanin ni na yi.
To wannan matsalar ce na samu wanda da aka zo aka fahimci juna sai aka yi ‘solving problem’ din. Kamar muryar Kairat Abdullahi kamar muryar Zubi Mu’azu.
” Mutane suna ta cewa muryar mu na dan yin kama saboda kin ga Umar duka yana yin wakoki da mu. To mutane wani lokaci Kairat idan ta dora Waka za a ce muryar Maryam Bakassi so ba ni bace. Sai wadanda suka asalin ni ce.
” Shi ya sa wani lokaci da aka gane matsalan haka ake yawan saka suna. Duk wace ta yi waka akan bata ‘credit’ din ta a ce Kairat Abdullahi, ko Maryam Bakassi, ko Zubi Mu’azu.
A karshe Bakassi ta ce ” Idan na yi aure zai ajiye sanar rerawaka ko da ko mijin da zan aura ya amince. Wannan shine burina idan Allah ya yarda.
Discussion about this post