Tsohon kakakin jam’iyyar APC, Yekini Nebena ya yi kira ga masu zargin ba a yi musu adalci ba wajen zaben mataimakin shugaba da Bola Tinubu yayi Musulmi cewa suma idan haka ne ai son kai ne suka yi domin shi masu addinin gargajiya ina sukuma za a ajiye su.
Nebena ya ce idan adalci ake magana, ina aka saka masu bin addinin gargajiya. Ko su ba mutane bane. Haka kuma gwamnonin yankin kudu da dukan su ‘yan addini daya ne, me suka tsinana wa mutane?
” Ai bai kamata ace wai saboda addini, ayi ta tada jijiyoyin wuya ba. APC ce ta yi abinda ya dace inda ta maida mulki yankin kudancin kasar nan. PDP wancakalar da tsarin tayi ta maida wa yankin Arewa da ke kai ta cigaba.
” Da gangar PDP ta yi watsi da tsarin karba-karba don ta dadada wa wani mutum daya da yankin sa, maimakon a nan ne mutane za su tada jijiyoyin wuya sai wadanda suka yi abinda ya dace, kawai dan abin ya zo akan gaba, dukkan su musulmai ne shikenan ba a yi daidai ba kenan.
Tun bayan da dan takarar shugaban Kasa na APC Bola Tinubu ya bayyana Kashim Shetima dan takarar mataimakin shugaban kasa, ake ta yin ceccekuce akai saboda dukkan su musulmai ne.
Kiristoci sun fito karara sun nuna adawarsu ga wannan zabi, inda wasun su suka ce ba za su bi tafiya Tinubu ba.
Sanata Abbo Elisha wanda dan jam’iyyar APC ne ya ce ba zai bi Tinubu ba a zabe mai zuwa.
Discussion about this post