Jami’an Gidan Kurkuku na shirin maida dakataccen Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Abba Kyari a hannun SSS, bayan wani yunƙurin kashe shi da aka yi a cikin kurkukun, wanda bai yi nasara ba.
Ba wasu ba ne su ka yi ƙoƙarin kashe shi a cikin kurkukun Kuje, sai waɗansu ɗaurarrun da su ka zarge shi da harƙallar riƙa karɓar kuɗaɗe a hannun masu laifi kafin ya sake su, a lokacin da ya ke bakin aikin sa.
Wasu bayanan da manyan jami’an kurkukun Kuje su ka fitar, waɗanda su ka faɗo hannun PREMIUM TIMES, sun tabbatar da cewa an kai wa Kyari hari a ranar 4 Ga Mayu.
Wani jami’i ya bayyana cewa kusan ɗaurarru 190 su ka kai masa harin, waɗanda mafi yawan su duk waɗanda aka tsare ne a cikin kurkukun saboda laifukan safarar muggan ƙwayoyi.
Ana tsare da Kyari a kurkuku bayan da jami’an NDLEA su ka maka shi kotu bisa zargin sa da harƙallar shigo da muggan ƙwayoyi a cikin Najeriya.
NDLEA ta kama Kyari ne bayan an dakatar da shi bisa zargin sa da alaƙa da kuma haɗa baki da gogarman ‘yan damfara, Hushpuppi su ka damfari wani Balarabe.
Zargin Da ‘Yan Ƙwayar Da Su Ka Kusa Kashe Kyari Ke Yi Masa:
Dandazon ‘yan ƙwayar da su ka kai wa Kyari hari a cikin Kurkukun Kuje ke yi masa, sun ce Kyari ya gabatar da su gaban kotu an hukunta su, duk kuwa da cin hancin maƙudan kuɗaɗen da suka riƙa ba shi.
Wata majiya a cikin masu bincike kuma ɗan leƙen asiri, ya bayyana mana cewa ai “Abba Kyari kura ce da fatar akuya.’
Shi dai Kyari har yau ya na nan kan bakan sa cewa bai aikata laifin komai ba.
Wata majiyar mu ta ce “Abba Kyari ya riƙa kakkaɓe ƙananan dillalan muggan ƙwayoyi, domin ya buɗe wa Afam Ukatu hanyar nasibin kasuwa.
Ukatu shi ne biloniyan dillalin muggan ƙwayoyi wanda aka kama ya shigo da ‘Tramadol’ na Naira biliyan uku cikin Najeriya, wanda Kyari ya dulmiya hannun sa a cikin harƙallar sa.
“Ɗaurarrun ‘yan ƙwayar sun yi iƙirarin cewa Abba Kyari zai nemi a ba shi cin hanci domin ya kashe maganar. Za su bayar da kuɗin, amma kuma zai maka su kotu a hukunta su.” Haka wata majiya ta shaida wa jaridar mu. Majiyar da ita aka zauna aka saurari ƙorafe-ƙorafen da ɗaurarrun ‘yan ƙwayar ke yi wa Kyari.
Kakakin Hukumar Gidajen Kurkuku na Ƙasa, Francis Enobore ya ƙaryata zargin an kai wa Kyari hari a cikin Kurkukun Kuje. Amma kuma PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa an kai masa harin, bisa hujjar bayanan da jaridar ta samu daga jami’an gidan kurkukun da kuma kwafen takardun bayanan da jami’an su ka rubuta bayan an kai masa harin.
Yadda Aka Keɓe Kyari A Wani Ɓoyayyen Wuri, Bayan An Sasanta Shi Da ‘Yan Ƙwayar Da Su Ka Nemi Halaka Shi:
Wata majiya ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa bayan an ƙwaci Kyari, an mayar da shi wani keɓantaccen wuri wanda babu wanda ya isa ya gan shi, kuma an tsaurara matakan tsaro sosai a wurin.
“Domin a yayyafa wa rigimar ruwan sanyi, sai da Kyari ya biya kowane ɗaurarren ɗan ƙwaya naira 200,000, don dai a kashe rigimar, a yi sulhu.
“Kuma ya sayi karin DSTV domin ɗaurarru su riƙa kallon tashoshin talabijin birjik su na ɗebe kewa a cikin kurkuku.” Inji majiyar PREMIUM TIMES.
Kyari dai ya tara dimbin dukiya da kadarorin da sun wuce hankalin albashin sa da alawus ɗin haƙƙin aikin sa da Gwamnatin Tarayya ke biyan sa.
A cikin Afrilu Hukumar NDLEA ta ce ta ƙwace manyan gidaje da gine-ginen sa da sauran kadarorin alatun maƙudan kuɗaɗe a Barno, Kano, Legas da Abuja.
“Ba Su Daina Barazanar Kashe Kyari Ba” -Majiyar Cikin Kurkuku:
Majiya a cikin kurkukun ta tabbatar da cewa ɗaurarrun ‘yan ƙwayar ba su daina barazanar kashe Abba Kyari ba. Su na cewa sai sun gano shi duk ma lungun da ake tsare da shi, sun kashe shi.
Majiyar ta ce yanzu haka sun bai wa Kyari wa’adin wani lokacin da su ka lallai ya biya kowanen su dukkan kuɗaɗen cin hancin da su ka taɓa ba shi.
Daraktan SSS Afunanya Peter bai amsa kiran da wakilin mu ya yi masa domin jin ta bakin sa ba.
Shi kuma Kakakin Gidajen Kurkuku na Ƙasa, bayan ya ƙaryata kai wa Kyari hari, ya ce bai san Kyari ɗin ya biya ɗaurarrun ‘yan ƙwayar naira 200,000 kowanen su ba.
Rayuwar Abba Kyari A Kurkukun Kuje:
Majiya ta ce jami’an kurkukun na cin moriyar zaman sa a can, domin ya na yi masu ihisani bakin gwargwado.
Majiyar ta ce “ya na da damar ganin matar sa, wadda ke kai masa ziyara. Kuma ba a ƙwace wayoyin sa ba. Sannan kuma malaman sa na zuwa wurin sa.”
Discussion about this post