A wata sanarwa wanda kakakin gwamna jihar Baeno Babagana Zulum ya saka wa hannu ya shaida cewa Kungiyar Boko Haram sun kashe mutum 32 a kauyen Madu dake karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.
Ya ce wannan abin takaici da tashin hankali ya auku ne a karamar hukumar Dikwa amma mutanen mazaunan Kala-Balge ne.
” Mutanen sun gamu da ajalinsu yayin da suka tafi balaguron neman karafuna a kauyen Mudu dake karamar hukumar Dikwa dake da nisan kilomita 45 da karamar hukumar Kala-Balge inda Boko Haram suka yi musu zobe suka kashe su.
“Mutum shida sun ji rauni a jikinsu a dalilin wannan farmaki sannan wasu mutum biyu sun tsira ba tare da rauni ba.
Gusau ya ce gwamna Zulum ya yi alhini da jajanta wa ƴan uwan waɗanda suka rasu.
“Akalla matasa 32 ne Boko Haram suka kashe yayin da suka je naman karafuna da aka fi sanin sa da Kayan Ajaokuta domin siyar wa masu aikin karfe.
“A ranar Talata sojoji da shugaban karamar hukumar Kala-Balge sun tsinci gawar mutum 14 da maharan suka daure suka harbe.
Gusau ya ce gwamnan ya aika da sakon jaje da ta’aziyya ga iyalai da mutanen karamar Kala-Balge.
Wannan hari ya zo ne a daidai mutane a jihar na cigaba da farincikin dawowar zaman lafiya a yankunan jihar da dama.
Discussion about this post