Tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu ya mika sakon taya murna ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kan nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar PDP.
A sakon taya murnar wanda Darektan Ƴaɗa labarai na kamfen ɗin Tinubu Bayo Onanuga ya saka wa hannu, Tinubu ya kara da cewa Atiku yana da jan aiki a gaban sa.
” Ina taya ka murnar lashe zaɓen fidda gwani da ka yi a jam’iyyar PDP. Idan komai ya ta fi yadda ake so, karshen ta da ni da kai ne za mu gwabza a zaben gamagari.
” Babban abinda ya rage maka kuma zai zame maka kashi a wuya shine yadda zaka wanke jam’iyyar PDP a idanu da zukatan ƴan Najeriya su manta yadda jam’iyyar ta yi ragaraga da dukiyar kasa a tsawon shekaru 17 da ta yi na mulki.
” Wannan shine babban aikin da ke gabanka. Domin ƴan Najeriya basu manta da yadda gwamnati PDP ta yi ragaraga da dukiyar kasar nan ba. Wannan shine zaka yi wa ƴan Najeriya bayani domin basu manta ba.
Tinubu na daga cikin ƴan takarar da ke kan gaba wajen neman jam’iyyar APC ta tsaida su ƴan takarar shugaban kasa.
Discussion about this post