Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi nasara a zaɓen fidda gwani na ɗan takarar shugaban kasa na PDP.
Da yake bayyana sakamakon zaɓen shugaban kwamitin gudanar da wannan zaɓe Sanata David Mark ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya samu kuri’u 371 in da ya doke sauran Ƴan takaran.
Atiku ya samu ƙuri’u 371, Wike 237, Udo, 38, Saraki 70. Bala Mohammed ya samu kuri’u 20.
Discussion about this post