Babban Faston cocin Katolika na jihar Sokoto, Mathew Kukah, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gama yin ragaraga da Najeriya, ya saka cikin halin ha’ulai.
A cikin jawabin da yayi a sakon bukin Easter Fasto Kukah y ace Najeriya bata taba fadawa cikin mawuyacin hali irin karkashin mulkin shugaba muhammadu buhari ba da za aci komai ya lalace in banda cin hanci da rashawa.
“ Mutane sun shiga halin kakanikayi, Iyalai sun fada cikin mawuyacin hali, masallatai da coci-coci sun ruguje, ilimi ya lalace, yara sun zama abin tausayi, siyasar Najeriya ta shiga rudu, tattalain arziki ya kakkarye, wutar lantarke ta zama gwal, maganan tsaro kuwa ya fi komai dagargajewa. Hanyoyin mu na motoci sun ragwargwabe basu biyuwa, layukan dogo ‘jiragen kasa’ sun zama bi da alwalanka, cin hanci da rashawa sun samu gindin zama a Najeriya duk a karkashin mulkin Buhari.
Kukah yace yanzu abin ya kai ga mutane sun shiga rudu, sun rasa gaban su sun rasa bayan su. Ba a san ida za a saka kai ba. “ Ba a san ko gwamnatin Buhari ta san halin da mutane ke ciki ba, su sa mutane na ganin kamar kila ma dai babu gwamnati ne a kasar ko kuma dai gwamnatin kanta ta shiga rudu ne bata san inda ta dosa ba.
fasto Kukah ya dade ya na ragargazar gwamnatin Buhari ba tun yanzu. Inda yake tsage gaskiya wajen bayyana lalacin gwamnatin da irin matsalolin da gwamnatin ta saka ‘yan Najeriya a ciki tun bayan darewar ta karagar mulki a 2015.