Wani abu kamar almara da ya auku a yau Lahadi shine yin sallama da jam’iyyar APC da tsohon gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari yayi ya koma PDP.
Yari ya koma PDP ne tare da illahirin magoya bayan sa kaf din su a jihar Zamfara.
Shugaban Jam’iyyar PDP, Bala Mande ne ya sanar da wannan gagarimin albishir ga yayan jam’iyyar PDP da yan Najeriya a garin Gusau da yake tattaunawa da manema labarai.
Mande ya ce ” mun tattauna da wakilan AbdulAziz Yari kuma mun amince da dukkan bukatun da suka zo mana da su. Yanzu dai an gama duk abinda za a yi, Da yari da Sanata kabiru Marafa duk sun tsunduma PDP.
Idan ba a manta ba, tun bayan canja sheka da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle yayi daga jam’iyyar PDP zuwa APC, aka fara zaman doya da manja tsakanin Yari da bangaren kabiru Marafa.
bangaren yari da Marafa ba su amince da jagorancin jam’iyyar wanda yakoma wajen gwamna Matawalle ba. A ganin su sune suka yanke wa APC cibi a Zamfara, suka yi mata bauta amma kuma Matawalle ya same ta rabas a jihar.