Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Najeriya na buƙatar a zuba mata Naira tiriliyan 348.1 domin ta cimma nasarar Shirin Bunƙasa Ƙasa na 2021-2025.
Buhari ya yi wanann bayanin a ranar Laraba, lokacin da ya ke ƙaddamar da shirin na National Development Plan na Shekaru Biyar.
Shirin dai ya zama ɗorawa ce zuwa mataki na gaba, daga Shirin Farfaɗo Da Tattalin Arzikin Ƙasa na 2017-2020, wanda wa’adin sa ya ƙare cikin Disamba, 2020.
Buhari ya ce ana buƙatar zuwa wannan jari na Naira tiriliyan 348.1 a cikin tattalin arzikin Najeriya, domin a samu ya bunƙasa da kashi 5 bisa 100 a tsawon shekaru biyar ɗin 2021-2022.
Idan aka samu haka, Buhari ya ce a cikin shekaru za a samar wa mutum miliyan 21 ayyukan dindindin, sannan kuma a ceto mutum miliyan 35 daga cikin talauci.
Ya ce shirin zai zama matakalar hawa tsanin fitar da mutum miliyan 100 cikin talauci, shirin da ya ce wannan gwamnatin ta sa gaba (National Poverty Reduction with Growth Strategy).
“Najeriya za ta yi ƙoƙarin zuba jarin Naira tiriliyan 49, wato kashi 14% na kuɗaɗen, yayin da kamfanoni za su zuba kashi 85.7%, wato Naira tiriliyan 293.3 kenan.
Buhari ya yi wanann jawabi a lokacin da gwamnatin sa ba ta iya samar da kuɗaɗen ayyukan kasafin kuɗaɗe sai ta ciwo bashi daga ƙasashen waje.
Wannan ne ya sa wasu da dama ke kallon abin kamar mafarki ko kallon-kawallalniya, wato ruwan-faƙo.
Discussion about this post