A daidai ƴan Najeriya na kokarin kai komo wajen neman abin dasu saka a bakin salati, da kuma zaman dardar da ake yi na hare-haren ƴan bindiga da ya addabi mutane a Najeriya, hukumar NCDC ta bayyana cewa akwai yiwuwar sake garkame kasar nan idan aka ci gaba da samun yawan waɗanda suka kamu da Korona a kasar nan.
Shugaban hukumar NCDC, Ifedayo Adetifa,ya bayyan cewa Korona ta yi ƙamari yanzu a kasar nan akwai yiwuwar gwamnati ta ɗau sabbin matakai a kasar nan.
A karon farko tun barkewar Korona a watan Faburairun 2020 Najeriya ta samu sama da mutum 4000 da suka kamu da cutar a rana ɗaya
” Mutane sun yi watsi da matakan kariya da a ka saka da suka haɗa da wanke hannaye, mulka man tsaftace hannaye, saka takunkumin fuska da yin nesa da juna, sannan kuma da rage cunkoso da taruka.
” Ba mu bukatar ace an kai ga har sai ƙasa ta ɗauki matakin da za a muzanta wa mutane amma kuma kiwon lafiyar mutane shine a gaban gwamnati.
Sai dai kuma ba a nan ne gizo ke saka ba domin wasu kwararru da suka tattauna da PREMIUM TIMES game da wannan niyya ta gwamnati sun ce haka nan dai gwamnati za ta ci gaba da hakuri da mutane amma saka dokar zaman Kulle ba zai yiwuba a Najeriya yanzu ba.
” Matsalolin da za a afka a ciki sun fi duk wani alfanu da za a samu idan aka garkame kasar.