‘Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kutsa a garuruwa biyu da ke cikin Ƙaramar Hukumar Faskari, su ka kashe mutane bakwai kuma suka yi garkuwa da wasu da dama.
Wani ɗan asalin yankin mai suna Lawal Mamman, amma ya na zaune a Katsina, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindiga sun dira ƙauyen Unguwar Ibrahim Maiwada da Kanon Haki wajen ƙarfe 9 na dare.
“Sun shiga Unguwar Ibrahim Maiwada tun wajen ƙarfe 9 na dare, amma ba su fita ba sai kusan asubahi. Da su ka fice ɗin ma, sai suka zarce ƙauyen Kanon Haki da ke kan babban titin Zariya zuwa Sokoto.
“Ɗan’uwa na ya kira ni ya ce min shi dai ya ga gawarwakin mutum biyar da aka kashe a Kanon Haki, sannan kuma sun raunata mutane da dama.” Haka Mamman ya shaida wa wakilin PREMIUM TIMES ta wayar tarho.
Sannan kuma ya ce an nemi wasu ‘yansakai su shida waɗanda su ka yi artabu da su, amma ba a gan su ba, har zuwa lokacin rubuta wannan labarin. Amma mutanen ƙauyen na fargabar cewa lallai zai yiwu an tafi da su, an yi garkuwa da su.
Wani mazaunin garin Unguwar Maiwada ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an kashe mutum biyu a garin, sannan kuma sun saci mata.
“Yansakai da su ka bi su sun ce mana maharan rabuwa su ka yi gida biyu lokacin da su ka fita daga Unguwar Maiwada. Wasu suka nufi Kanon Haki domin kai farmaki, wasu kuma su ka nausa cikin daji da mata biyar ɗin da suka kama.” Inji majiyar mu.
Wakilin mu ya kasa jin ta bakin Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Katsina, Gambo Isa, saboda bai amsa kira ba, kuma bai maida masa amsar saƙon tes da ya yi masa ba.