Akalla mutum 189 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya daga ranar Litini zuwa Talata.
Hukumar NCDC ta ce a takanin wadannan ranaku mutum uku ne suka mutu a dalilin kamuwa da cutar.
A ranar Litini mutum 90 ne suka kamu, mutum daya ya mutu
Mutum 99 ne suka kamu, mutum daya ya mutu ranar Talata
A jimla mutum 212,150 ne suka kamu, an sallami mutum 203,524, har yanzu mutum 5,600 na dauke da cutar sannan mutum 2,899 sun mutu a kasar nan.
Idan ba a manta ba alkaluman sakamakon gwajin cutar da hukumar ta fitar ranar Lahadi ya nuna cewa mutum daya ya mutu sannan mutum 74 sun kamu da cutar.
Yaduwar cutar
Legas – 77850, Abuja-23,276, Rivers-12,707, Kaduna-10,031, Filato-9,790, Oyo-8,742, Edo-6,594, Ogun-5,373, Kano-4,360, Akwa-ibom-4,338, Ondo-4,545, Kwara-3,930, Delta-4,096, Osun-3,006, Enugu-2,761, Nasarawa-2,517, Gombe-2,579, Katsina-2,212, Ebonyi-2,048, Anambra-2,346, Abia-2,017, Imo-2,053, Bauchi-1,727, Ekiti-1,771, Benue-1,809, Barno-1,344, Adamawa-1,136, Taraba-1,250, Bayelsa-1,243, Niger-1,056, Sokoto-796, Jigawa-604, Yobe-501, Cross-Rivers-645, Kebbi-458, Zamfara-302, da Kogi-5.
Bayan haka gwamnatin jihar Legas ta ce asibitoci masu zaman kansu za su rika karbar kudi daga masu zuwa yin rigakafin Korona, sai dai kuma kyauta za rika yi a asibitocin gwamnati.
Sanwo-Olu ya ce gwamnati ta hada hannu da asibitocin masu zaman kansu domin a yi wa mutum miliyan 4 rigakafin korona daga yanzu zuwa ranar 25 ga watan Disemba.
Burin gwamnati shine yi wa akalla kashi 30% na mutanen jihar allurar rigakafin korona nan da shekara daya.
Zuwa yanzu gwamnati ta yi wa mutum miliyan 1.2 allurar rigakafin korona a jihar.
Sanwo-Olu ya ce gwamnati da hukumar NPHCDA zasu hada hannu da asibitoci masu zaman kansu domin a kara yawan wuraren da ake yi wa mutane rigakafin Korona a jihar
Discussion about this post