Idan ba a manta ba a ranar Talata ne babbar Kotun Shari’a da ke Kaduna ta yanke hukuncin kamfanin jaridar Today ta biya gwamnan Kaduna zunzurutun kuɗi har naira miliyan 10 diyyar yi masa ƙazafi da jaridar tayi masa.
Jaridar ta buga labari a 2015 cewa wai gwamna El-Rufai ya bayyana makudan kuɗi har naira biliyan 90 da wasu kantama-kantaman gidaje har 40 a matsayin kadarorin da ya mallaka kafin ya zama gwamna.
El-Rufa’i na karban kudaden da Kamfanin Today ta biya ya bada su kyauta wa asusun da aka bude domin dawainiyar da nakasassu a jihar.
Shugaban kungiyar JONAWD Suleiman Abdulazeez ya sanar da haka da yake mika godiyarsa ga gwamnan kan kyautar da ya yi wa kungiyar ranar Talata.
Abdulazeez ya ce El-Rufa’i ne mutum na farko da ya fara zuba kudi a asusun da aka bude domin kula da nakasassu a jihar, karkashin wannan kungiya.
“Hakan da gwamnan ya yi ya nuna kauna da kokari da gwamnati ke yi wajen ganin ta inganta rayuwar masu fama da nakasa a jiki.
Bayan haka sakataren hukumar kula da masu fama da nakasa ta jihar Kaduna Aliyu Yakassai ya ce kyautar da gwamnan ya yi ya zo bayan hukumar aiyukan jinkai da ingata al’umma Hajiya Hafsat Baba, ta gabatar da kudirin bude asusun domin kula da masu nakasa a jikinsu wa kwamitin zantarwa na jihar ranar Litinin.
Ya ce hakan da gwamnan ya yi na nuna alamun kyawawan shirin da gwamnati ta ke da shi domin inganta rayuwar masu nakasa a jikinsu a jihar
Yakassai ya ce nan bada da dadewa ba asusun za ta fara aiki sannan gwamnati za ta shirya taro domin mutane da kungiyoyin bada tallafi na ciki da wajen jihar su bada nasu gudunmawar wa asusun.
Bisa ga dokar nakasassu kamata yayi gwamnati ta bude asusun domin kula da al’amuran masu fama da nakasa a jikinsu.
Gwamnati za ta kafa hukumar wace za ta rika kula da shiga da fitan kudade domin kula da nakasassu.
Discussion about this post