Sabon Ministan Harkokin Lantarki da Makamashi, Abubakar Aliyu ya shiga dabur-dabur da inda-inda, lokacin da ya kasa kare ba’asin yadda za a kashe naira biliyan 42 a cikin kasafin ma’aikatar sa na 2022.
Aliyu wanda ya zama Ministan Harkokin Lantarki cikin watan Satumba, bayan cire Saleh Mamman, kafin hawan sa shi ne Ƙaramin Ministan Ayyuka da Gidaje.
Yayin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lantarki da Makamashi, Minista Abubakar Aliyu ya bijiro da batun za a kashe naira biliyan 42 a aikin tashar wutar Zungeru, kuma ya kira aikin cewa sabon aiki ne za a yi.
Sai dai kuma nan da nan ɗaya daga cikin ‘yan kwamiti, kuma Shugaban Marasa Rinjaye, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya taka masa burki tare da sacce masa tayoyi.
Abaribe ya yi mamakin yadda Minista Abubakar ya kira aikin tashar wutar Zungeru a
Matsayin sabuwa, alhali kuma tuni har an kashe wa aikin naira biliyan 25 cikin kasafin 2021.
“Ta yaya kuma Minista zai kira tsohon aikin da har an fara shi a cikin kasafin 2021, kuma ya lashe naira biliyan 25?” Inji Abaribe.
Sauran mambobin sun nuna damuwa su ma, tare da cewa ko a kasafin kuɗin 2021 sai da aka tayar da ƙura a gaban wannan kwamiti kan waɗannan kuɗaɗe.
Ganin yadda ya kasa bada cikakkar amsa, Minista Abubakar ya bada haƙuri, ya ce kalmar “sabo” da ya furta, kuskuren keken rubutu ne.
Daga nan kuma duk wata tambaya da su ka sake yi masa, sai a jefa ta ga babban jami’in kula da ɓangaren da ake neman bayani a wurin sa.
Ministan ya gabatar da Kasafin 2022 na naira biliyan 301.