Tsohon gwamna Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana cewa bai san gwamna Abdullahi Ganduje na aika masa da sakon murnar zagayowar ranar haihuwar sa ba.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da sashen Hausa na BBC ranar Asabar.
Tun da farko an tambayi Kwankwaso ko ya ga sakon taya murnar cikarsa shekaru 65 da gwamna Ganduje ya aika masa, sai ya ce bai gani ba domin aiki ya masa yawa.
” Aiki yayi min yawa, ban samu na zauna ba ballantana in san haka.In da haka yake yi tuntuni da ba haka ba, duk wanda ya sanni ba wanda zai zo ya ce ya fadi wani abu a kan Ganduje na saurare shi, domin dukkaninsu Kwamishinoni sun sani da sauran ma’aikata da mutan gari, domin idan kace mutum yana da laifi daya amma yana da dai-dai guda tara sannan kace za ka kalle shi da wannan laifin ai ka ga akwai matsala”
” Na zauna da mutane lafiya ciki har da Ganduje, haka muka bar gwamnati muka koma ma’aikatar tsaro, haka muka yi tsari ya tafi Chadi, haka kuma yana can na ce ya sauka ya dawo gida mu yi aiki da shi, ya dawo na dauki fom din mataimakin gwamna na bashi, na ce kai ne babba, ba tare da ko sisin Kwabo ba, domin mu a tsarinmu na Kwankwasiyya ba wanda zai ce ka bada ko sisin Kwabo”
Sai dai Kwankwaso, ya yi zargin cewa duk da waɗannan abubuwa da ya yi wa tsohon mataimakin nasa, yanzu da shi Ganduje ke fito na fito da adawa fiye da kowa.
Gaba ɗaya tarihin siyasar Kwankwaso tare da Ganduje suka yi shi, a koda yaushe ya kan neme shi ya zo su yi aiki tare kuma yana bashi girma.
Yayi wa Kwankwaso mataimakin gwamna a farko daga shekarar 1999 zuwa shekara 2003 sannan daga shekara 2011.
Discussion about this post