WUTSAN WARKI MAI JAYE-JAYE: Dalilan cire Nanono, ministan gonar da ya ce Najeriya ba a san yunwa ba

0

A ranar 21 Ga Agusta, 2019 Majalisar Dattawa su ka amince da Mohammed Sabo Nanono a matsayin minista daga cikin ministocin da Shugaba Muhammadu Buhari ya miƙa masu sunayen su domin su tantance.

Sai dai an cika da mamaki, ganin yadda Nanono ya rika dawurwura da dabur-dabur a Majalisar Dattawa a lokacin da ya ke gabatar da kan sa.

Kawunan ‘yan Najeriya ya ƙara ɗaurewa ganin yadda wasu sanatoci makusantan sa su ka hana a yi masa tambayoyi, sai dai a ka ce ya je ya rusuna ya yi gaisuwa ya ƙara gaba.

Sanatocin sun nunke ‘yan Najeriya baibai, inda su ka ce Nanono mutum ne masanin harkar noma na yankan-shakku. Alhalin digirin sa na farko ma ba a fannin noma ya yi shi ba. A fannin kasuwanci ya yi.

Nanono: Tsohon Gari A Cikin Sabon Gora: Tun bai daɗe da haɗawa Ministan Harkokin Harkokin Noma ba, Sabo Nanono ya nuna cewa zamani ya yi masa nisa, ya tsere masa fintinkau.

Da ya ke magana a kan matsalar yunwa a Najeriya, tun farkon naɗa shi, ya ce ƙaryar yunwa ake yi a Najeriya.

“Yan Najeriya kukan daɗi da kukan shagwaɓa su ke yi. Babu wata yunwa a Najeriya. Ni na ga yadda ake yunwa a Indiya a wani zuwa da na yi cikin 1973.”

Nanono ya ce ya kamata Najeriya ta ma taimaka wa ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi wajen bunƙasa masu harkokin abinci.

Nanono: Wutsan Warki Mai Jaye-jaye:

Minista Sabo Nanono ya ƙara janyo wa kan sa tsangwama da hayayyaƙa a lokacin da a cikin watan Yuni, 2020 ya yi bushawar yi wa farin-ɗango feshin naira biliyan 13.

Feshin dai a jihohi 12 Nanono ya ce za a yi shi, kuma tun ma kafin farin su ƙaraso Afrika ta Yamma.

Jihohin da ya ce za a yi feshin tun kafin farin su ƙaraso, sun haɗa da Katsina, Kaduna, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Jigawa, Bauchi, Barno, Adamawa, Bauchi da Taraba.

Wannan kalami ya janyo masa tsangwama sosai a faɗin ƙasar nan.

Akwai bangarori da ake ganin Nanono ya samu nasara a fannin bunƙasar harkokin noma a ƙasar nan, sai kuma inda gizo ke saƙar, abincin da ake tutiyar ana nomawa, bai hana kayan abincin tsula tsada ba, kuma bai hana shigo da kayan abinci daga waje ba.

Sannan kuma biliyoyin kuɗaɗe da ake rabawa da sunan lamunin noma, jama’a da dama na ƙoƙarin cewa ba su isa ga manoman gaskiya, yawanci manoman biro ke ramce kuɗaɗen.

Ƙaiƙayin baki ya kai Nanono cewa a daina kukan yunwa a Najeriya, domin shi ya san akwai inda a Kano mutum zai iya cin abincin naira 30 ya ƙoshi.

Tun ana jin haushin sa a kan wannan katoɓara da ya yi, har an koma ana yi masa dariya da ba’a da barkwanci da kuma shegantaka.

Ko tsige shi da Shugaba Buhari ya yi, an riƙa yin shegantaka a Kano, ana cewa ya dawo gida ya buɗe gidan cin abincin naira 30.

Satar Rashin Mutunci A Ma’aikatar Gona:

A wani dogon binciken yadda jami’an gwamnati ke sata asiri rufe, PREMIUM TIMES ta fallasa yadda aka maka naira biliyan 3.08 a cikin aljifan ma’aikatan Ma’aikatar Harkokin Noma su 42 a cikin watan Satumba zuwa Disamba, 2021.

Kwana ɗaya bayan tsige Minista Nanono. Shin Allah ya raka nono gona za a ce kenan ko kuwa?

Share.

game da Author