KORONA: Ba a gama jimamin mutum 14 da Korona ta yi ajalin su ranar Talata ba, ta sake dauke mutum 11 ranar Alhamis

0

Hukumar NCDC ta bayyana cewa cutar korona ta yi ajalin mutum 11 sannan mutum 582 sun kamu ranar Laraba a Najeriya.

Hukumar ta ce an gano wadannan mutane a jihohi 15 da Abuja.

Cutar ya ci gaba da yaduwa yayin da gwamnati ke kokarin tilasta mutane wajen yin allurar rigakafi a kasar nan.

A jimla mutum 193,013 sun kamu mutum 2,480 sun mutu.

An sallami mutum 173,492 sannan mutum 11,533 na dauke da cutar

Korona Ranar Talata

Idan ba a manta ba hukumar NCDC ta bayyana cewa mutum 14 ne suka mutu, mutum 626 sun kamu a kasar nan ranar Talata.

Sannan a ranar Litini mutum 460 ne suka kamu mutum 1 ya mutu.

Yaduwar cutar

Legas – 73,093, Abuja-20,624, Rivers-10,591, Kaduna-9,237, Filato-9,205, Oyo-8,156, Edo-5,462, Ogun-5,262, Kano-4,050, Akwa-ibom-4,028, Ondo-3,968, Kwara-3,562, Delta-2,971, Osun-2,711, Enugu-2,558, Nasarawa-2,414, Gombe-2,258, Katsina-2,164, Ebonyi-2,048, Anambra-2,075, Abia-1,794, Imo-1,710, Bauchi-1,553, Ekiti-1,466, Benue-1,423, Barno-1,344, Adamawa-1,136, Taraba-1,071, Bayelsa-1,062, Niger-966, Sokoto-796, Jigawa-564, Yobe-501, Cross-Rivers-476, Kebbi-458, Zamfara-251, da Kogi-5.

Tilasta mutane yin allurar rigakafin korona a Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta hukunta duk wadanda suka ki yin allurar rigakafin korona.

A ranar Talata shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya sanar da haka a taron da ya yi da manema labarai.

Shuaib ya ce gwamnati za ta yi “amfani da tsarin doka” a kan mutanen da suka ki yin allurar rigakafin saboda za su jefa rayuwar wasu mutane cikin hadari.

Idan ba a manta ba a wannan mako ne

Babbar Kotun Fatakwal da ke Jihar Ribas ta dakatar da Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo daga ƙaƙaba dokar hana shiga masallatai da coci-coci sai da katin shaidar rigakafin korona.

Obaseki ya saka dokar hana mutane shiga masallatun, coci-coci, manyan kantuna da sauran wuraren da mutane ke taruwa idan ba sun nuna katin shaidar yin allurar rigakafin korona ba.

Kafin gwamnati ta fara yi wa mutane allurar rigakafin gwamnati ta shaida wa mutane cewa ba za ta tilasta mutane yin allurar rigakafin korona ba amma za ta wayar da kan mutane kan mahimmancin yin allurar rigakafi.

Share.

game da Author