Fadar Shugaban Ƙasa ta yi wa Amnesty International dirar-mikiya, inda fadar ta ce ƙungiyar ‘Amnesty International’ ta koma goyon bayan ‘yan ta’adda. Don haka ba ta da hujjar haƙƙi da ‘yancin ci gaba da zama cikin Najeriya.”
Kakakin Fadar Shugaban Ƙasa Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Shehu ya yi wannan kakkausan bayani ne a matsayin raddi, bayan ‘Amnesty International’ ta roƙi Gwamnatin Najeriya ta kawo ƙarshen yadda mutane ke ɓacewa a rasa inda su ke a ƙasar nan.
‘Amnesty International’ ta yi ƙoƙarin yadda mutane ke ɓacewa musamman a kudancin ƙasar nan a ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi a daƙile ‘yan taratsin IPOB da Neja Delta.
Sai dai kuma a cikin kakkausan martanin da Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar, Garba Shehu ya zargi AI da goyon bayan kungiyoyin da su ka ɗauki makami su na faɗa da gwamnati.
“Irin yadda Amnesty International ke goyon ‘yan ta’adda irin su Nnamdi Kanu da IPOB, duk da an haramta su, ya nuna cewa su na ta haƙilo ne don kawai ƙasashen yamma su karɓe su hannu bibbiyu.
“Duk duniya an ga yadda ‘yan ta’addar IPOB ke kashe ‘yan sanda, su ƙone ofisoshin su, su ƙone dukiyoyin gwamnati. Amma Amnesty International ba ta ga laifin wannan babban laifi ba. Ta yi biris ta kauda kai.
“Da a ƙasashen su ne na Turai hakan ke faruwa, za su rika suka da kawo hujjojin wajibcin yaƙar su.” Inji Shehu.