Dagula ƙwaƙwalwar mitar wutar lantarki na kawo mana cikas wurin tara kudin shiga a jihohin Kano, Jigawa da Katsina – Hukumar Wutar Lantarki

0

Hukumar wutar lantarki dake kula da jihohin Kano, Jigawa da Katsina ta koka kan yadda mutane a jihohin ke dagula mitar wutar lantarki ta yadda ba za su rika siyan wuta yadda ya kamata ba.

A wata takarda da aka raba wa manema labarai ranar Juma’a a garin Kano darektan yada labarai na hukumar Ibrahim Sani-Shawai ya bayyana cewa wannan matsala na hana hukumar samun kudaden shiga yadda ya kamata.

Sani-Shawai ya ce mutum 17, 190 a wadannan jihohi basu biyan kudaden wutar lantarkin da suke amfani da shi daga watan Janairu zuwa Yulin 2021.

” Hakan da mutane ke yi na kawo mana cikas a wuraren samun kudaden shiga.

“Duk da haka mun amince mu samar da wutan lantarki wa mutane kamar yadda gwamnati ta bada umurni.

Bayan haka Sani-shawai ya yi gargadin cewa akwai hadarin gaske hakan da mutane keyi a wadannan jihohi.

Ya ce daga yanzu hukumar za ta rika hukunta duk wanda ta kama yana satar wutar lantarki bisa ga tanadin dokar kasa.

Sani-shawai ya yi kira ga mutane da su kai karar duk wanda suke gani yana kaucewa biyan kudin wutar lantarki a unguwan su.

Share.

game da Author