Yadda matar makwabci na ta gaggaura min mari a gabar mata ta don ta ga ko za ta rama min – Wani likita a Abuja

0

Wani likitan dabbobi mai shekaru 37, Akor Kenneth, ya bayyana wa Kotun Yankin Grade I, dake Kubwa dake Abuja cewa wata makwabciyarsa mai suna Juliana Umana ta gaggaura masa mari a gabar matarsa da mijinta don ta ga ko matar tasa za ta rama masa.

‘Yan sanda sun kama Juliana bisa laifin cin zarafin makwabci.

Lauyan da ya shigar da karar Babajide Olanipekun, ya ce Kenneth wanda ke zama a hanyar Arab Road, Kubwa, ya bayyana cewa Juliana ta gaggaura masa mari ne a lokacin da yake tattaunawa da wasu daga cikin makwabtansa kan yadda za su bude hanyar ruwa da ya toshe a cikin gidan da suke haya.

” A ranar 10 ga Nuwamba, 2020 yayin da muke tattaunawa da sauran makwabtan mu game da matsalar da ake fama da shi na toshewar hanyar ruwa da ya ratsa ta gidan su sai Juliana ta matso kusa da ni ta gaura min mari a gaban mijinta da wasu makwabtan mu biyu.

“Juliana ta gaura min mari ne saboda sun taba dambe da mata ta, shine ta huce akai na, inji magidanci a Kotu.

Kenneth ya ce ya kauce daga wannan wuri ya shige gida kada fushi ya kwashe shi ya yi wa juliana lugugen kulli, saboda ko da ta gaura masa mari ko a jikinta balle ta bashi hakuri.

“Rashin bani hakuri da Juliana da mijinta suka ki yi ya sa na kai karar ta ofishin ‘yan sanda.

Alkalin kotun, Muhammad Adamu ya dage shari’an zuwa ranar 10 ga Satumba.

Share.

game da Author