KATSINAWA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Mahara sun bi gida-gida kamar ‘yan tashe, sun yi kisa, sun yi gaba da shanu 300

0

Wasu mahara sun yi wa ƙauyen Kukar Babangida dirar-mikiya cikin dare a ranar Lahadi, inda su ka kashe magidanci ɗaya tare da jikkata wasu mutum uku.

Majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES Hausa cewa maharan sun riƙa bi gida-gida kan su tsaye, ba tare da fargabar ko jami’an tsaro za su kai ɗauki ba. Sun riƙa shiga wannan gida zuwa wancan kamar ‘yan tashe, su na kwasar duk wata dukiya mai amfani da su ka ci karo da ita.

“Sun kashe mutum ɗaya, wanda aka yi wa jana’iza a yau Litinin. Wasu uku da aka ji wa rauni kuma su na asibiti. Sun riƙa kwasar shanu, babura da sutura.”

Majiyar da ba ta so a ambaci sunan ta, ta tabbatar da cewa bayan maharan sun tafi, an lissafa sun yi gaba da shanu kimanin 300 da babura da sutura masu yawa.

Ƙauyen Kukar Babangida an sa masa sunan Shugaban Mulkin Soja Ibrahim Babangida ne, saboda ya tsaya ƙauyen ya dasa bishiya, a wata ziyara da ya kai Katsina a lokacin da ya ke mulki.

Wakilin mu ya kira lambar wayar Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Gambo Isa don ji ƙarin bayani, amma bai same shi ba.

Katsina ta da wasu jihohin Arewa Maso Yamma na ci gaba da fama da hare-haren ‘yan bindiga babu kakkautawa.

Share.

game da Author