‘Yan sanda sun kama wasu ma’aurata da suka yi karyar yin garkuwa da dayan su a jihar Neja

0

Rundunar ‘yan sanda jihar Neja ta kama wani magidanci mai suna Mohammed Mohammed da matarsa Sadiya da laifin karyar yin garkuwa da dayan su sannan suka sanar wa ‘yan sanda.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Wasiu Abiodun ya sanar da haka a garin Minna a makon jiya.

Abiodun ya ce Mohammed da matarsa Sadiya mazauna karamar hukumar Chanchaga ne sannan ‘yan sanda sun kama su ranar 22 ga Yuli a Limawa cikin garin Minna.

Ya ce rundunar ta samu labarin cewa an yi garkuwa da Sadiya a tsohuwar hanyar zuwa tashar jiragen sama dake Minna bayan ta taso daga wajen aiki ranar 15 ga Yuli.

“Daga nan wadanda suka yi garkuwa da Sadiya suka kira mahaifin ta inda suka bukaci ya biya Naira miliyan 5 kudin fansa. Sai dai kuma bayan tattaunawa da aka yi da su mahaifin Sadiya ya biya naira miliyan ɗaya.

Abiodun ya ce a ranar 21 ga Yuli bayan Sadiya ta dawo gida sai rundunar ta gaiyyace ta zuwa ofishinta domin amsa wasu tambayoyi.

“Garin amsa wadannan tambayoyi Sadiya ta tona asirin abinda ya auku wa jami’an tsaron cewa ita da mijinta ne suka shirya a yi garkuwa da ita na karya domin su samu kudi.

Ya ce Mohammed da Sadiya na tsare a ofishinsu sannan za a kai su kotu da zaran rundunar ta kammala yin bincike.

Idan ba a manta ba a ranar 8 ga Mayu ne mahara suka sace ɗaliban Islamiyyar Salihu Tanko a Tegina da ke Ƙaramar Hukumar Rafi a Jihar Neja.

kada a kirkure a kashe yaran.”

Ya ƙara da cewa gwamnati na ƙoƙarin bin wata hanyar sako yaran ba tare da an biya diyya ba.

Sai dai kuma a ranar Lahadi.

Yan bindigar da su ka sace yaran Islamiyar Tegina sun riƙe dattijon da aka aika kai kuɗin fansa naira miliyan 30, bisa zargin cewa kuɗin ba su cika cif-cif ba.

Share.

game da Author