RASHIN TSARO: An kashe mutum 201, an sace mutum 137 a makon jiya

0

A makon da ya gabata an ƙididdige yawan mutanen da aka kashe a hare-hare da dama a faɗin ƙasar nan, sun haura mutum 200.

Sannan kuma an samu ƙididdige yawan mutum 137 da aka sace, aka yi garkuwa da su.

An samu adadin ne daga rahotannin jaridu da sauran kafafen yaɗa labarai ke wallafawa da kuma jin ta bakin iyalan mamata da na waɗanda aka yi garkuwa da su.

Tun a ranar waccan Lahadi ce ‘yan bindiga su ka bindige Ahmed Gulak a Owerri, babban birnin Jihar Imo. Gulak tsohon Mashawarcin Goodluck Jonathan ne a fannin siyasa. Amma ya koma jam’iyyar APC tun kafin zaben 2019.

A Jihar Ebonyi ma ‘yan bindiga sun kashe mutum 30 a garuruwan Odoke, Ndiobasi da Obakotara cikin Ƙaramar Hukumar Ebonyi.

A ranar Litinin Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya bakwai, ta hanyar ɗana masu nakiya a kan hanyar da su ke wucewa, a Jihar Barno.

Duk a cikin makon da ya gabata ɗin ne dai aka tafka gumurzun yaƙin da sojojin Najeriya su ka hana dakarun ISWAP shiga Damboa, su ka karshe fiye da 50.

Dakarun ‘yan ta’addar ISWAP sun sha wuta a hannun sojojin Najeriya, lokacin da su ka yi wani mummunan shirin afkawa garin Damboa, a Jihar Barno, a ranar Laraba, 2 Ga Yuni.

Sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Rundunar Sojojin Najeriya, Mohammed Yerima ya fitar, ya bayyana cewa sojojin Najeriya sun fatattaki ‘yan ta’adda, kuma su ma kashe fiye da 50.

Ya ce sun darkaki Damboa da mummunan shiri, inda su ka nemi kai farmaki a cikin ƙatuwar motar yaƙi mai sulke da kuma motocin daukar manyan bindigogin harbo ƙananan jiragen yaki, kowace ɗauke da bindigar tashi-gari-barde.

“Akwai kuma wasu motocin maƙare da dama-bamai da nakiyoyi, sai kuma wasu garken ‘yan ta’adda a kan baruwa.”

Ya kara da cewa sojojin Najeriya sun yi masu hawan-ƙawara, inda su ka da ‘yan ta’addar ISWAP fiye da 50 zuwa barzahu.

ISWAP dai su ne hatsabiban bangaren Boko Haram da su ke balle daga Boko Haram, su ka yi wa Shekau tawaye. Daga nan su ka nemi haɗin kai da goyon bayan ISIS.

A cikin makon jiya ne rahotanni su ka cika duniya da labarin kisan Shekau a hannun ‘yan ISWAP, tare da damƙe wasu manyan kwamandojin sa da dama.

Tuni dai har sabon Babban Hafsan Najeriya, Manjo Janar Yahaya ya jinjina wa sojojin Najeriya, bisa wannan gagarimar nasara da su ka samu a kan ISWAP.

Ya kuma ƙara masu jinjina da zaburaswa cewa su ci gaba da matsa-lamba da matsa-ƙaimin ƙarasa murƙushe ‘yan ta’adda baki ɗaya.

A Jihar Neja gwamnati ta tabbayar da cewa daliban Islamiyya 136 ne aka yi garkuwa da su.

Gwamamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa adadin ɗaliban Iskamiyyar da masu garkuwa su ka sace a garin Tegina na Jihar Neja, su 136 ne.

Mataimakin Gwamnan Neja, Ahmed Ketso ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke ƙarin bayani dangane da halin da ake ciki a jihar tun bayan kwashe ɗaliban da aka yi a farkon makon jiya.

Ketso ya tabbatar wa iyayen ɗaliban cewa gwamnati na yin dukkan bakin ƙoƙarin ganin an cefo ɗaliban sun koma gidajen su cikin ƙoshin lafiya.

Ya kuma yi bayanin irin motocin sintirin da gwamnatin jihar ta sai wa jami’an tsaro, har da babura.

Domin ƙarfafa matakan tsaro a jihar, gwamnatin jihar Neja ta haramta haya da baburan achaba a cikin Minna, babban birnin Jihar Neja.

Da ya ke ƙarin bayani, Mataimakin Gwamna, Ahmed Ketso ya ce kada a ƙara ganin baburan ‘okada’ na karakaina a cikin garin Minna.

Haka su ma masu baburan kan su na hawan yau da kullum, an taƙaita zirga-zirgar su, daga ƙarfe 9 na dare zuwa wayewar gari, ƙarfe 6 na safiya.

Haka kuma gwamnati ta umarci dukkan Hakimai da Dagatai da Masu Unguwanni su tabbatar sun riƙa tantancewa, ƙididdigewa da yi wa kowane baƙon da ya sauka cikin al’umma rajistar sanin asali, tare da damƙa bayanan sa a hannun ‘yan sanda da sauran jami’an tsaron da ke da kusanci da jama’a.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda ‘yan bindiga sun kashe mutum 88 a Kebbi.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da kisan mutum 88 da ‘yan bindiga su ka yi a cikin Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu ta Jihar Kebbi.

Rundunar ‘yan sandan ta ce lamarin ya faru a ranar Alhamis, kuma akwai yiwuwar waɗanda aka kashen sun haura haka, domin har zuwa ranar Asabar an nemi wasu mutanen ba san inda su ke ba.

Kakakin Yaɗa Labarai na Rundunar ‘Yan Sandan Kebbi, Nafi’u Abubakar ya ce maharan sun tsallako ne daga maƙwautan jihohi wato Zamfara da Neja, domin a iya sanin su babu wani sansanin ‘yan bindiga a Jihar Kebbi.

Abubakar ya lissafa ƙauyukan da ‘yan bindigar su ka kashe mutane, sun hada da Koro, Kimpi, Gaya, Dimi, Zutu, Rafin Gora da Igenge.

Wannan bala’i ya afka wa Jihar Kebbi makonni biyu bayan kifewar da jirgin ruwa ya yi inda ya halaka mutane masu tarin yawa.

A ranar Juma’a kums ‘yan bindiga sun bindige mutum 9 a Magami da Mayaba, cikin Karamar Hukumar Gusau ta Jihar Zamfara. Manoma ne aka kashe a lokacin da su ke sharar gonakin su, domin shirin fara noman daminar bana.

Share.

game da Author