Sanin kowa ne daga jiya zuwa yau Musulmai a wannan kasa sun shiga rudani da rikicewa marar misaltuwa, akan rashin tabbas na ganin watan Shawwal. Wanda ganin shi shine abun da kadai zai ba da damar sauke azumi a fara hidimar Sallah karama a yau ranar laraba da ace angan shi jiya ranar talata. Al’amarin sai ya zo da turka-turka da sammatsi haryayi sanadiyar rarrabuwar kan Al’ummar musulmi a wannan kasa!
A wannan rana ta laraba hakika Musulman wannan kasa ta Najeriya sun tashi cikin wani hali na rashin tabbas na yi yuwar ajiye azumi ko kuma cigaba da yin azumi. Wannan abu ina mai tabbatar wa mai karatu cewa ba abune da duk Musulmi mai kaunar cigaban musulunci ne zai ji dadin hakan ya cigaba da faruwa ba, domin wannan yana kawo rarrabuwar kawunan Musulmi ne a idon duniya.
Maikaratu zai san cewa shi ganin wata wani abune da ya ke da tsari a addinin musulunci. Wanda ake tabbatar da ganin sa idan adalai a cikin mutanen gari suka tabbatar da ganin sa (Watan). Ko kuma jama’a masu dan yawa (Kamar mutum 5 haka) su tabbatar da ganin wannan watan. Babu kokonto sun gani idan wadannan mutane suka cika ka’idoji da duk wasu tambayoyi idan akai musu suka tabbatar da cewa sun ga wata.
Amma idan muka koma kan yadda Sarkin Musulmi yake rikon sakainar-kashi da wannan mas’alar ganin watan za muga cewa kullum abun kara gaba yakeyi maimakon ya ragu a dinga samun hadin kai na musulmi amma abun ya ci tira. Kuma wannan ba zai rasa mas’ala da rashin samun wasu gamsassun bayanai daga bakin mai-alfarma sarkin musulmai ba. Wanda hakan babban illace shugaba ya kasance mai nauyin baki wajan bayyanawa Al’umma abun da yake musu kaikayi.
Musulmai da yawa na tuhumar Sarkin Musulmi da zargin bin tsarin kasar saudiya ba tantagaryar tsarin addinin islama ba. Wannan zargi ne da ya kamata sarki ya gamsar da Al’ummar kasa domin ya wanke kansa daga wannan zargin, kuma ya cire shakku daga zukatan Al’umma.
Babbar matsalar da shugabanni na Africa ke samu ba iyaka na addini ba shine, rashin gwanancewa wajan iya cusawa Talakawan su yarda da su, kamar yadda bature ke cewa ‘building of trust’. Wannan shi ke bayuwa wajan talakawa su yi wa shugabanni tawaye.
Maganar gaskiya akwai yiyuwar tabbacin cewa wadanda suka ajiye azumi a yau sun fi wadan da suka cigaba da azumi dacewa da gaskiya. Duba da yawan kauyukan da akace anga watan a jiya talata a sassan wannan kasa — wanda sun kai wajan kauyuka ashirin da doriya. Amma ni da na yi wannan rubutu na kasance a cikin masu yin azumi a wannan rana ta laraba, domin yin biyayya ga shugabancin Sarkin Musulmi na wannan Kasa tamu Najeriya. Saboda nasan cewa duk wani nauyi na daukar Alhaki ko akasin haka zai koma kansa ne ba kaina ba, kamar yadda yake a koyarwar Alkur’ani da sunna.
Wannan matsaya tawa ta yadda da umarnin Sarkin Musulmi ba shi ke nuna munfi wadanda suka ajiye azumi tun jiya gaskiya ba, domin annabi ba cewa ya yi abi sarkin Musulmi ba cewa yayi “Idan kunga wata Ku dauki azumi idan kuma kunga wata ku sauke”. Shi ya sa dole mu ja hankalin masu zargin wadan da suka ajiye ba dai-dai bane. Hakazalika, ba dai dai bane zagin wadanda suka bi umarnin sarki, domin bin umarnin shugabanni yana da asali a cikin addinin islama.
Kuma wannan shekarar tsarin na yiwa sarki tawaye ya zo da sabon salo irin na Damon karbuwa daga ko wanne bangare (Izala, Tijjaniyya, Qadiriyya da Shi’a). Gaskiya yin hakan ba karamar barazana ce ga shi mai alfarma Sarkin Musulmi ba.
Shiyasa ya zama wajibi ayiwa wannan mas’ala kallo na tsanaki da duba mai zurfi domin ayiwa tufkar hanci. Kodai sarki ya kara dagewa wajan fahimtar da Al’umma domin su fahimce shi ko kuma shi ya fahimci Al’umma domin samun maslaha. Saboda kullum hadin kan Al’umma shine abun so (Wahadatul-ummah). Allah ya kara hadakan Musulmi ba ki daya, ameeeeen.
Khalid Sunusi Kani mai fashin baki ne akan al’amuran yau da kullum kuma dan gwagwarmaya ne daga Kano. Za ku iya samun shi kamar haka: 07030631259 email: Drkani01@yahoo.com
Discussion about this post