Fursinoni 115 sun ci darussan Turanci da Lissafi a Jarabawar NECO na bana

0

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da gidajen yari ta kasa dake jihar Enugu Monday Chukwuemeka ya bayyana cewa wasu fursinoni 115 sun ci darussan Turanci da lissafi a jarabawar NECO na shekarar 2020 da aka yi a jihar.

Chukwuemeka ya fadi haka a garin Enugu a zantawa da yayi da manema labarai.

Hukumar jarabawar NECO ta fitar da sakamakon jarabawar ranar 7 ga Mayu 2021.

Chukwuemeka ya ce a shekarar 2018 fursinoni 84 ne suka ci darussan Turanci da Lissafi, kuma a shekarar 2019 fursinoni 136 ne suka ci darusan Turanci da lissafi a jihar.

Ya ce hukumar gidan yari na horas da fursinoni da koyar da su karatun boko a lokacin zaman su a gidajen.

Share.

game da Author