KWAN-GABA-KWAN-BAYA: Yayin da Gwamnatin Buhari ke dukan kirjin gamawa da Boko Haram, a lokacin su ke kara kafa sansanoni a wasu jihohi

0

Duk da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta sha yin ikirarin cewa an kakkabe Boko Haram, saura ‘yan burbushin da ke kai hare-haren sari-ka-noke a Arewa maso Gabas, to kalaman wasu gwamnoni a kwana-kwanan nan sun sanya tsoro da damuwa a zukatan jama’a da ma gwamnatin ita kan ta.

Tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Tukur Buratai ya sha bayyana cewa an kakkabe Boko Haram a Najeriya. Wadanda ake yaki da su a yanzu, gaggan ‘yan ta’addar ISWAP ne.

ISWAP, wato ‘Islamic State of West Africa’, su ne ke jidalin yakin ganin sun kafa shari’ar musulunci a kasashen Afrika ta Yamma.

ISWAP asalin su mayakan Boko Haram ne da su ka balle bayan samun baraka da Boko Haram.

Su biyun sun haddasa mutuwar fiye da mutum 20,000 daga shekarun 2009 zuwa yau.

Ba sojojin Najeriya su Buratai kadai su ka yi ikirarin kakkabe Boko Haram ba, jami’an gwamnatin Buhari sun sha fitowa su na sanarwar kakkabe Boko Haram, kamar irin yadda Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed a cikin 2019 ya ce:

“Mun samu nasarar yin galaba a kan Boko Haram, an kakkabe su daga cikin kasar nan. Yanzu wadanda ake fama da su, wani sabon rikici ne da wasu ‘yan ta’addar da su ka buwayi duniya (ISWAP).

“Wasu bangaren Boko Haram sun hade da gawurtattun ‘yan ta’addar ISIS, daga nan su ka kafa ISWAP. Kenan a halin yanzu ISIS ta kafu a Afrika ta Yamma, inda a Najeriya nan ne babban fagen dagar da ake gumurzun yaki da su.

“Fatattakar da aka yi wa ISIS a Iraq da Syria ta haifar da karkato muggan makaman su a hannun ISWAP.

“Kenan sojojin mu su na yaki ne da dandazon mayun ‘yan ta’adda na duniya, wadanda sun ci dubu. Kuma wadannan ‘yan ta’adda su ne fa sojojin Najeriya ke gwagwagwar yaki da su, ba tare da sa hannun sojojin gamayyar duniya da su ka hada da sojojin Amurka ba.” Inji Lai.

Bayan shekaru shida da Buhari ya shafe a kan mulki, maimakon hare-haren Boko Haram su ragu, sai ma karuwa su ke yi har a cikin Maiduguri da wasu sassa na jihohin Najeriya, wadanda ba su ma da makautaka da jihar Barno.

An samu rahoton hare-haren Boko Haram, kamar yadda Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya shaida wa Shugaba Muhammadu Buhari a cikin watan Janairu.

Haka kuma baya bayan nan an samu rahoton sun kafa sansani a jihar Neja, har sun kwace gari guda sun kwace matan garin sun aure a tsakanin su.

Cikin Afrilu ma an samu rahoton bullar Boko Haram a wasu Kananan Hukumomi hudu na Jihar Bauchi, har Gwamna Bala da Badaru na Jihar Jigawa su ka kwartsa kururuwar bullar su.

Ranar Lahadi da gabata, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Sheikh Ahmad Gumi ya ce bindigar da su ka saci daliban Jami’ar Greefield a Kaduna, su na da alaka da Boko Haram.

Fitaccen malami Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa ‘yan bindigar da su ka yi garkuwa da daliban Jami’ar Grenfield ta Jihar Kaduna, sun ki sakin su saboda ‘yan bindigar na da alaka da Boko Haram.

Gumi ya yi wannan furuci a wata hira da ya yi da Channels Television a ranar Lahadi, a Kaduna.

‘Yan bindigar dai sun saci dalibai 20 daga Jami’ar Green Field, wadda ke kan titin Kaduna zuwa Abuja a ranar 17 Ga Afrilu, kuma zuwa yanzu sun kashe biyar daga cikin su.

Sun kuma yi barazanar kashe sauran idan ba a biya su diyyar naira miliyan 100 ba kafin su sake su.

A hira da Gumi ya ce ba kamar garkuwar da ake yi da mutane a yankin Arewa maso Gabas ko Arewa maso Yamma ba, “su wadanda zu ka sa ci daliban su na da alaka da Boko Haram a cikin dajin.

“Wannan ne karon farko a garkuwa da mutane inda mu ka tabbatar da alaka tsakanin ‘yan bindiga da Boko Haram. Hakan ya nuna yadda Boko Haram ke kara kutsowa, kuma hakan gagarimar matsala ce.” Inji Sheikh Gumi.

Gumi ya kara da cewa ‘yan Boko Haram sai da su ka tuntubi ‘yan bindigar da su ka saci daruruwan dalibai a sakandaren Kankara ta Jihar Katsina, har su ka nemi su sayar masu da dukkan daliban, domin sun tabbatar za su rubanya riba a wurin tattauna sakin su.

Sai dai Gumi ya ce ‘yan bindigar ba su amince da tayin da Boko Haram su ka yi masu ba. Sun saki dukkan daliban bayan sun cimma sasantawa tsakinin su da Gwamna Matawale na Zamfafa.

“To amma tattauna sakin sauran daliban Greenfield University abu ne mai wuyar sha’ani, saboda alakar ‘yan bindigar da Boko Haram.” Cewar Gumi.

Share.

game da Author