Ban yi mulki don na ci zarafi ko tozarta mutane ba -Jonathan

0

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana cewa mulki wani zango ne mai takaitaccen wa’adi, don haka ba mukami ba ne da mutum zai rika amfani da shi ya ci zarafi ko ya azabtar da mutane ba.

Jonathan ya yi wannan furuci ne a Benin, babban birnin Jihar Edo, wurin taron taya Shugaban Cocin Rock of Ages Christian Assembly Charles Osazuwa murnar cikar haihuwar sa shekaru 50.

“Ni dama can abin da na yi amanna da shi tun kafin na shiga siyasa, na kudirta a rai na cewa mulki ko mukami ba abu ne tabbatacce ba. Wani wa’adi ne na wucin gadi Ubangiji ya bai wa mutum . Don haka ba zan yi amfani da shi na ci zarafin jama’a ba.” Inji Jonathan.

Tsohon shugaban na Najeriya wanda ya yi wa marigayi Shugaba Umaru ‘Yar’Adua mataimaki kafin zaman sa shugaba daga 2010 zuwa 2015, ya kara da cewa ana tunawa mutane ne da abin da su ka shuka a baya.

“Daga cikin abubuwan da na yi a lokacin da na ke kan mulki, har ake tunawa da ni, shi ne ba zan taba amfani da mukami na har na haddasa musabbabin kisan wani ko wasu ba.

“Duk wani mukami da na rike bisa hukuncin ubangiji a kan kaddara, ba zan yi amfani da shi ya zama silar kuntatawa ko azabtar da kowa ba.” Cewar Jonathan.

Daga nan ya ci gaba da yaba wa limamin cocin bisa gudummawar da ya ke bayarwa wajen inganta rayuwar jama’a da dama.

Cikin wadanda su ka yi jawabai a wurin, har da Gwamnan Jihar Edo, Gidwin Obaseki, sai kuma Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta.

A na sa jawabin, shugaban cocin, Okowa ya yi kira ga ‘yan siyasa su rika rige-rigen inganta rayuwar masara galihu.

Okowa ya buga misali da irin yadda Annabi Da’uda ya rika inganta rayuwar marasa galihu.

Share.

game da Author