KORONA: Sunayen Mutane 90 Da Najeriya Ke Farauta, Bayan Sun Shigo Daga Indiya, Kasar Da Sabuwar Cutar Korona Ke Wa Mutane Kisan Rubdugu

0

Gwamnatin Najeriya ta buga sunayen mutum 90, wadanda su ka kunshi Indiyawa 27 da ‘yan Najeriya 63, wadanda su ka shigo Najeriya ba tare da bin ka’idar tsayawa a killace su tsawon kwanaki bakwai ba kamar yadda dokar ta tilasta wa wanda ya shigo kasar nan daga Indiya, Brazil ko Turkiyya.

A ranar 1 Ga Mayu,2021 ne Kwamitin Dakile Cutar Korona ya sanar da sabuwar dokar cewa duk fasinjan da zai sauka Najeriya daga Indiya ko Brazil ko Turkiyya, tilas ne a killace shi tsawon kwanaki bakwai, kafin a bar shi ya shiga cikin garuruwan Najeriya.

Bijiro da wannan doka ya biyo bayan bullar sabuwar samfurin cutar korona mai yawan kisan mutane birjik musamman a Indiya da Brazil.

Wadanda Najeriya ke cigiya din su 90, an sanar cewa ba su bari an killace su tsawon kwanaki bakwai din ba, kuma tuni shige cikin garuruwan kasar nan, ana mu’amala da su.

‘Kowa Ya Yi Kaffa-kaffa Da Wadannan Mutane 90’ -Gwamnatin Najeriya:

Sanarwar da Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa, kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana mutanen su 90 a matsayin babbar barazana ga rayuka da kiwon lafiya a Najeriya. Don haka a yi kaffa-kaffa da su, kuma a kai rahoto.

Ya kara da cewa sun shigo ne ta filayen jiragen saman Abuja da na Lagos a ranakun 8 Ga Mayu da kuma 15 Ga Mayu, 2021.

Sun shigo ne ta jiragen zirga-zirga na Ethiopean Airline da kuma Qatar Airline.

Sanarwar ta kuma nemi su gaggauta kai kan su ga hukumomin kula da lafiya wadanda aka sanar masu.

An kuma buga lambobin waya guda biyu da za su buga domin a yi masu karin bayani.

Gwamnatin Tarayya ta kuma bayyana cewa za a hukunta su kamar yadda doka ta tanadar, tare da hana su fita kasashen waje na wani tsawon lokacin da bai gaza wa’adin shekara daya ba, ko fiye da haka.

SUNAYEN MUTUM 90 DA AKA CE KADA ‘YAN NAJERIYA SU MATSA KUSA DA SU:

Sunayen Indiyawan Da Su Ka Shigo Najeriya Ba Bisa Ka’ida Ba:

Abha Jalandhar Punjab, Ajaya Kumarmurali, Kapil Shikarpur Uttarpradesh, Chandra Dakshya, Vekwa Dinesh Kumar

Thatill Tijo George, Anand Amit Kumar, Puthussery John Joseph, Rathore Babu Lal, Umesh Narayan Kotian, Kabid Shauna, Ramesh Rao, Biswal Naresh, Puthussery John Joseph, Mukherjee Sobhan, Birla Mahesh Kumar, Mishra Ajay Kumar, Mishra Shlok, Mihsra Nanjari, Bendre Abhijit Bhagwan, Shah Jignesh, Dogra Sumit, Pradhan Bharat Chandra, Chandan Kumar Pandey, Kaur Armin, Francis Micky and Pokale Honaji.

Wadanda Su Ka Shigo Ta Filin Jirgin Nnamdi Azikwe na Legas:

Imojire Charles Edemhenmhen, Shittu Olamide Hammed, Niguri Elizabeth T. and Oviasuyi Osage Brown.

Akwai kuma Ogunsanya Omotola S., Chioma Ebeh, Gerald Chukwuma Anyadigibe Adedapo-Aisida Oluwayemisi, Obi Tochukwu Bright, Ajibade, Temitope, Abdulsalam Yusuf, Umezurike Bernard, Passos Okori, Obi John, Unaje Chuks, Eluke Aaron, Mogbonjubolataiwo, Adesina Adeola Kudirat, Adesina Abdulselem O, Onukwube Ericm, Okonkwo Chukwuebuka, Lebura Agefachuwku, Obidi Chukwud, Onyekwelu Dumebi, Anakpe Reuben, da sauran su.

Share.

game da Author