Buhari ya amince da shirin farfado da Rugagen Tsugunar da Makiyaya Wuri Daya

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a farfado da Shirin Zaunar Da Makiyaya a Rugage wuri daya, domin a magance matsalar fadace-fadacen makiyaya da manoma a fadin kasar nan.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya sa wa hannu, ya ce ana nan ana ci gaba da nazarin tsare-tsaren shirin domin a magance kalubalen da ake samu daga makiyaya masu rike da muggan makamai.

Wannan sanarwa ta biyo baya ne kwanaki kadan bayan ilahirin gwamnonin jihohin Kudu 17, har da na APC a cikin su, sun haramta gararambar kiwon shanu a jihohin su.

Cikin makon da ya gabata kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa hana makiyaya kiwon da gwamnonin Kudu su ka yi, ya kauce wa dokar Najeriya.

Din haka Malami ya ce gwamnonin ba su da ikon haramta kiwo a jihohin su.

Haka shi ma Shugaba Bihari ya bayyana cewa gwamnonin sun yi azarbabi, kuma sun yi riga-malam-masallaci.

Garba Shehu ya bayyana cewa, ‘Shugaba Buhari na da tsare-tsaren ganin an kawo karshen wannan matsala baki dayan ta.

“Ministan Harkokin Noma Sabo Nanono ya bijiro wa Shugaba Buhari da tsare-tsaren tsugunar da Fulani wuri daya.”

Ya ce tun ma a cikin watan Afrilu Buhari ya amince, kafin ma gwamnonin kudu su fito da sanarwar hana kiwo a jihobmhin su.

Ya ce hana kiwo da gwamnonin su ka yi akwai siyasa cikin lamarin.

Buhari ya ce kokarin da gwamnoni ke yi na haramta kiwo, ba zai magance matsalar ba.

Sai dai kuma ya ce al’ummar jihohin da aka hana kiwon su na da hakkin da shugabannin su za su samar musu tsaro, to amma ba ta hanyar fitowa a haramta kiwo sakaka ba.

Ya ce dokar Najeriya ta bai wa kowa ‘yancin walwala da yin rayuwa a inda ya ke son zama.

Sanarwar ta ce duk inda aka kafa rugagen tsugunar da Fulani makiyaya, za a samar mazu asibitin duba lafiyar dabbobi, samar da makarantu ga ‘ya’yan Fulani da sauran kayan more rayuwa.

Share.

game da Author