CIGIYAR KUDADEN DA AKA KWATO DAGA 2002-2020: Majalisa ta gayyaci jiga-jigan gwamnatin yanzu da gwamnatocin baya

0

Kwamitin Majalisar Tarayya Mai Binciken Kashe Kudaden Satar da Gwamnati ta Kwato, ya gayyaci wasu jiga-jigan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma jiga-jigan gwamnatocin baya, daga 2002 zuwa 2020.

An gayyace su ne ana bukatar su fara bayyana daga ranar Litinin din nan, domin yin bayanin yadda aka kashe kudaden da ake kwatowa daga hannun barayin gwamnati.

Majalisar Tarayya ta nuna damuwa ganin cewa duk da yawan tulin makudan kudaden da gwamnatin Buhari ke kwatowa, amma a kullum sai gagararambar fita kasashe neman ciwo bashi gwamnatin ke yi.

A karkashin Gwamnatin Buhari, Majalisa ta gayyaci Ministan Shari’a, Abubakar Malami, sai Ministar Kudade Zainab Ahmed, sai Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris, Babban Mai Binciken Kudade na Kasa, Arhotomhenla. An kuma gayyaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

An kuma gayyaci Shugabannin Hukumomin NDLEA, NSCDC, SIA, EFCC, ICPC, NPF, NCS da Hukumar Sojojin Ruwa.

A bangaren gwamnatocin da su ka shude kuwa, an gayyaci Tsoffin Ministocin Shari’a, Masu Bai Shugabannin Kasa Shawara a Fannin Tsaro, Shugabannin EFCC, ICPC, IGPs sai Tsoffin Shugabannin Kwastan.

Shugaban Kwamitin Bincike Adejoro Adegun, dan APC daga Jihar Ondo, ya bayyana cikin wata sanarwa a ranar Lahadi cewa kwamitin sa na so ya san ko tantagaryar nawa ne adadin kudaden da aka kwato ko aka karbo tun daga 2002 zuwa 2020.

Kuma ya na so ya san adadin kadarorin da aka karbo ko aka kwato a cikin wadannan shekaru.

Ya kara da cewa za su yi haka ne domin tabbatar da cewa ana kashe kudaden ta hanyoyin da su ka dace.

Kwamitin ya kuma yi rika ga ‘yan Najeriya su rubuto masa kasidu kamar yadda Sashe na 88 da na 89 na Kundin Dokokin Najeriya na 1999 ya shimfida.

Idan ba a manta ba, cikin watan Janairu, 2020 Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya ce Najeriya ta kwato Naira biliyan 800, kuma an gurfanar da mutum 1,400 a kotu.

Sai dai kuma yawan kudaden da Najeriya ke karbo wa ba su rage wa Najeriya yawan ciwo bashi ba.

Cikin watan Agusta, 2020 sai da SERAP ta rubuta wa Shugaba Buhari wasikar neman yi wa ‘yan Najeriya bayani dalla-dalla na yadda gwamnatin sa ta kashe kudaden da ta kwato, har naira biliyan 800. Amma dai Buhari bai yi cikakken bayanin ba.

Amma a ranar 12 Ga Disamba, ranar Dimokradiyya, Buhari ya sanar a jawabin sa a takaice cewa an kwarara makudan kudaden ana ta yin ayyukan raya kasa da su.

Share.

game da Author