JIGAWA: Hisbah ta kama kwalaben giya 308 a Gumel

0

Rundunar Hisbah dake jihar Jigawa ta kama kwalaben giya 308 a karamar hukumar Gumel.

Shugaban Hukumar na jihar Ibrahim Dahiru ya sanar da haka ranar Asabar a garin Dutse.

Ya ce hukumar ta kama kwalaben giya ranar Juma’a a wani Otel dake Gujungu da karfe 10 na dare.

“Sai dai dakarun hukumar bata yi nasarar kama masu siyar da giyar ba. Duk sun gudu a lokacin da suka hangi ma’aikata sun kawo hari Otel din.

Dahiru ya ce rundunar za ta damka kwalaben giyan ga rundunar ‘yan sandan jihar domin ci gaba da bincike.

“Shan giya, siyar da ita da kuma safarar ta, laifi ne a Jihar Jigawa, saboda haka hukumar bazata yi kasa a guiwa ba wajen ganin an dai na siyar da giya a jihar da kuma yaki da wasu laifuffuka masu kama da haka.

Idan ba a manta ba a watan Maris PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda jami’an Hisbah suka kama mota dankare da jarkoki da kwalaben giya a karamar hukumar Kazaure.

Rundunar ta kama jarka 25 cike makil da giya a wata mota kirar Tayota Corona da kuma kwalabe na giya 364 bayan ta samu bayanan sirri dangane ga jigilar kayan giyar a karamar hukumar ta Kazaure.

Hisbah ta farfasa kwalaben giya har kimanin 2,875 da kuma jarka hudu na Burkutu a samame da ta kai wasu wurare da dama da ake kwankwadar giya a fadin Jihar.

Share.

game da Author