SALWANTAR NAIRA BILIYAN 4.1 A MAJALISA: SERAP ta rubuta wa Lawan da Gbajabiamila wasikar gorin sata

0

Kungiyar Bin Diddigin Yadda Ake Kashe Kudaden Gwamnati Bisa Ka’ida (SERAP), ta rubuta wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila wasika cewa su yi amfani da mukaman su su binciki salwantar naira biliyan 4.1 a Majalisa, sannan su damka wadanda ake zargi ga hukumar dakile rashawa da cin hanci.

Makudan kudaden dai an yi zargin cewa sun salwanta ne ko dai ta hanyar karkatar da su, ko facaka da su, ko kuma cancak aka sace su.

Kudaden wadanda tun a cikin 2016 aka ware su domin a yi ayyuka da su a Majalisa, amma ba a yi aikin ba, Ofishin Akanta Janar na Tarayya ne ya bayar da rahoton salwantar kudaden.

Wasikar wadda SERAP ta aika kuma ta sa hannu a ranar 15 Ga Mayu, ta na dauke ne da sa hannun Mataimakin Darakta Kolawole Oluwadare.

“Daya daga cikin aikin majalisa shi ne su tabbatar sun toshe hanyoyin zamba da karkatar da kudaden hakkin al’umma. Amma idan ya kasance majalisa ba ta iya tunkarar wannan kalubale a cikin ta, to babu wani abin kirkin da za iya hasalawa.”

SERAP ta kuma yi kira ga Lawan da Gbajabiamila su gano ‘yan majalisa da ma’aikatan majalisa wadanda su ka karkatar ko su ka sace kudaden, a cunna masu hukumar EFCC domin a gurfanar da su kotu, a hukunta su.

“Idan ku ka yi haka, za a tabbatar da cewa jama’a ku ke yi wa aiki kenan, ba berayen bariki ba.”

Ba Kunya Ba Tsoron Dauri: Dalla-Dallar Yadda Aka Yi Jigila Da Jidar Naira Biliyan 4.1 A Majalisa:

1. Akanta Janar na Tarayya ya bada rahoton cewa naira biliyan 4,144,706,602.68 sun salwanta a Majalisa a cikin 2016.

2. Majalisa ta biya wasu ‘yan kwangila naira miliyan 417.3 ba tare da rattaba hannu a kan ko da takardar tsire ba.

Akanta Janar ya nemi Jami’in Gudanarwa na Majalisa ya karbo kudaden daga hannun ‘yan kwangilar.”

3. “Majalisa ta kashe naira miliyan 625 a karkashin Kwamitin Tantancewa Bibiyar Dokoki tsakanin Maris zuwa Yuni, 2016, ba tare da gabatar da ko takardar kunshe balangu ba.

Su ma wadannan kudade Akanta Janar ya ce ‘Clerk’ na Majalisa ya karbo kudaden a hannun ‘yan kwamiti, kuma ya bayar da takardar shaidar karbo kudaden.

4. Akwai wasu naira miliyan 66.7 da aka ce majalisa ta kashe kudaden a kan ma’aikatan ta. To amma sunan wadanda aka rubuta an kashe wa kudaden, ba na su sunayen ba ne a takardar da banki ya fitar na wadanda aka kashe wa kudaden.

5. Akwai wasu naira miliyan 116, naira miliyan 56.9, wasu naira miliyan 126.2, sai naira miliyan 747.2, naira miliyan 118.6, naira miliyan 109, wasu naira miliyan 821.5, naira miliyan 254 da kuma wasu naira miliyan 375.8 da sauran kananan miliyoyin da rahoton ya ce an karkatar ko an sace, kuma aka nemi a maido su.”

Wannan wasika dai SERAP ta aika kwafe-kwafen ta zuwa ga Ministan Shari’a Abubakar Malami, Shugaban ICPC, Bolaji Owasanoye, Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa da Shugabannin Kwamitocin Bin Diddigin Kashe Kudade na Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya.

Share.

game da Author