Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana cewa ba zai saka dokar hana yawon kiwo a jihar har sai ya samar da wuraren da za a rika killace dabbobi suna kiwo a fadin jihar.
Bello ya fadi haka ne a lokain da yake hira da talbijin din ‘Channels TV’ ranar Juma’a.
Ya ce bai ga dalilin da zai sa ya kori dumbin Fulani makiyaya da suka dade suna zama a jihar kamar yadda wasu jihohin Kudancin kasar nan suke yi ba, shi ba zai yi haka ba.
Ya ce gwamnati tare da hadin gwiwar masarautun gargajiya, manoma, matasa, mata da maza sun tsara hanyoyin da zasu taimaka wajen samar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma a jihar kafin gwamnati ta samar da wurin da makiyayan za su rika kiwon dabobbin su.
“Duk wani shawara da gwamnati za ta dauka game da kawo karshen wannan matsala ana yi tare da makiyaya Fulani da manoma a jihar.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda Gwamnonin kudancin Najeriya 17 suka saka dokar hana yawon kiwo a jihohin su 17.
Wannan matsayi da suka dauka ya biyo bayan ganawa da gwamnonin suka yi ne a garin Asaba, babbar birnin jihar Delta.
Gwamnonin yankin kudu sun dade suna zaman doya da manja tsakanin su da fulani makiyaya da suka bazu a yankin suna yawaon kiwo.
Suna zargin fulani makiyaya da tada zaune tsaye a jihohin na su sannan kuma da yin ikirarin sune ke ruruta rashin zaman lafiya a jihohin su musamman tsakanin makiyaya da manoma.
Discussion about this post