Gwamnoni sun amince su fara zartas da cin gashin kan kotuna da Majalisun Dokoki cikin mako mai zuwa – Minista Ngige

0

Gwamnonin Najeriya sun amince da yarjejeniyar da su ka cimma da ‘ya’yan kungiyar JUSUN masu yajin aiki da kuma bangaren ma’aikatan Majalisar Dokoki, domin fara aiki da tsarin cin gashin kan bangarorin biyu daga hannun gwamnonin jihohin kasar nan.

Wata sanarwa daga Ma’aikatar Kwadago ta Tarayya ce ta sanar da haka a ranar Juma’a.

Sanarwar ta bayyana cewa an cimma wannan matsayar amincewa da fara aiki da tsarin cin gashin kan kotuna da majalisun dokokin jihohi ne bayan an yamutsa gashin baki da tayar da jijiyoyin wuya a taein da aka yi da shugabannin ma’aikatan kotuna a ranar Alhamis, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sanarwar wadda Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatatar Kwadago, Charles Akpan ya sa wa hannu, ta ce Minista Chris Ngige ya ce za a fara aiki da sabuwar yarjejeniyar a mako mai zuwa.

Ngige ya ce ma’aikatan JUSUN za su janye yajin aikin su da zarar an fara aiki da tsarin a mako mai zuwa.

JUSUN ta fara yajin aiki tun a ranar 6 Ga Afril, inda su ka kulle dukkan kotunan kasar nan, shari’u su ka tsaya cak a manya da kananan kotuna.

Haka su ma kungiyar Ma’aikatan Majalisar Dokoki sun (PASAN) sun shiga wannan yajin aiki domin neman a bai wa majalisa cin gashin kan ta.

Minista Ngige ne ya jagoranci ganawa da JUSUN da PASAN a ranar Alhamis. A wurin taron akwai Sakataren Kwamitin Tsarin Cin Gashin Kan Kotuna da Majalissun Dokoki, Ita Enang, wanda kuma shi ne mashawarcin Shugaba Buhari kan Harkokin Neja Delta.

Duk da gwamnoni ba su wurin, Ngige ya ce sun amince da matsayar da aka cimma.

Share.

game da Author