Shugaban Jami’ar Covenant University da ke Ota, Jihar Ogun, Fasto David Oyedepo, ya bayyana cewa lalacewar matasa a yanzu ta kai makurar maleji, yadda ba su tunanin komai sao dai su yini su na kwana su na danne-dannen wayoyi da hirarrakin banza a soshiyal midiya (chating).
Oyedepo wanda ya yi wa matasa wannan bulala, ya yi furucin ne wurin yaye dalibai a Bukin Saukar Karatu a 15 na jami’ar, a Ota, jihar Ogun.
“Zamani guda ya wanzu wanda matasan cikin sa sun zo duniya a banza, za su kuma bar duniyar a wofi ba tare da sun tsinana wa kan su komai ba. Hankulan su ya karkata wajen danne-dannen waya, ba su tunanin kirkiro wani ci gaban kam su ko na al’umma. Ba su ma da lokacin yin tunanin.”
Oyedepo ya ce yawan bata lokaci ana hirarrakin banza da wofi a soshiyal mediya ya sa matasa sun baude daga kan hanyar da alheri da arzikin da su ka zo nema a duniya.
“Soshiyal midiya ta yi wa matasa shamaki daga samun alherin da su ka zo duniya su samu. Sun makance, ba su san inda duniya ta sa gaba ba. Kuma ‘yan danne-dannen wayar banza ya cinye masu lokacin da za su iya yin tunanin amfana wa kan su ko amfana wa al’umma.
“Maimakon a ce sosbiyal midiya ta zama alheri a wurin su, to sharri ta zame masu, saboda ta cinye masu lokacin da za su yi tunanin kirkiro abin arzikin da za su iya yi har su zama wata tsiya.
“Idan ba ka san inda za ka ba, ba za ka taba isa inda ya kamata ka karasa ba. Sai dai ka yi ta gararamba da bilumbituwa.”
Oyedepo ya shawarci matasa su tashi tsaye, kuma su zama jajirtattu. Ya ce su gaggauta fitowa daga cikin akurkin da su ka kakaba kan su a ciki.