KISAN SHEKAU: Gwamnatin Amurka ba za ta biya ladar dala miliyan 7 ga kungiyar ISWAP ba

0

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ba za ta biya ba za ta biya ladar dala miliyan 7 ga kungiyar ta’addancin ISWAP da Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya mutu a hannun su ba.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Abubakar Shekau ya mutu a hannun dakarun ISWAP, wadanda su ka yi masa kofar-raggo tare da wasu kwamandojin sa, a cikin Dajin Sambisa.

Ya mutu ta hanyar tada wa jikin sa bom, bayan an shafe tsawon lokaci ana tattauna cewa ya yi mubayi’a shi da dakarun sa ga ISWAP.

ISWAP sun balle daga Shekau cikin 2016, su ka hade kai su da ISIS, sun kai wa sansanin Shekau harin mamaya ce ta hanyar amfani da manyan motocin yaki.

Ladar Dala Miliyan 7:

Cikin 2020 ne Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa za ta biya ladar dala miliyan 7 ga duk wanda ya bayar da bayanin da aka yi amfani da shi aka yi nasarar kama Shekau.

Sai dai kuma cikin wata sanarwa da bayan mutuwar Shekau din, Amurka ta ce wadannan makudan daloli ga ISWAP ba, kungiyar da ke karkashin ISIS.

“Rahotanni a yau sun nuna Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya dana wa kan sa bam ya kashe kan sa, a lokacin fadan su da kungiyar da ke da alaka da ISIS.

“To ku ‘yan ISIS mu na sanar da ku cewa ba za mu ba za a ba su kudin ba, domin ba haka tsarin biyan ladar ya ke ba.”

Sai dai kuma wani abin mamaki kisan Shekau bai ja hankalin ‘yan Najeriya da dama ba.

Dalili na farko dai jama’a sun gaji da jin labarin an kashe Shekau, domin a baya an sha bada labarin cewa ya mutu. Amma daga baya sai ya fito ya karyata.

Share.

game da Author