GASKIYAR LAMARI: Dalilan dakatar da Shugabar Hukumar NPA, Hadiza Bala-Usman

0

Kwafen wasu takardun da su ka fado a hannun PREMIUM TIMES sun tabbatar da an dakatar da Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa (NPA), Hadiza Bala Usman domin ta kauce a samu Kamfanin Binciken Kudade da zai binciki asusun NPA tare da bin-diddigin kudaden da NPA ta tara wa Gwamnatin Tarayya, tsakanin 2016 lokacin da aka nada Hadiza, har zuwa karshen shekarar 2020.

Wata wasikar da Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ya aika wa Shugaba Muhammadu Buhari tun a ranar 4 Ga Maris, 2020, ya yi masa korafin cewa: “kudaden da NPA ta tara a karkashin Hadiza tsawon shekarun da ta yi a hukumar, kwata-kwata ko kadan ba su kai adadin da ya kamata a ce an tara ba.”

A cikin wasikar Amaechi ya ce an kasa zuba wa asusun Gwamnatin Tarayya zunzurutun naira biliyan 165 (N165, 320, 962, 697).

A dalilin haka ne Amaechi ya shawarci Buhari cewa a binciki asusun Hukumar NPA.

Raddin Hadiza:

A cikin amsar da ta rubuta wa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari a ranar 5 Ga Mayu, 2021, Hadiza ta ce tsari, turba, mataki da ma’aunin da Ofishin Kasafin Kudi ya bi domin bayyana kudaden da Hukumar NPA ta kamata ta zuba a cikin asusun Gwamnatin Tarayya, duk cike su ke da tasgaro. Sannan kuma tsarin bai fi hanyar da Dokar Wajibcin Tara Kudaden Shiga ga Gwamnatin Tarayya ba, wato ‘Fiscal Responsibility Act’.

Hadiza ta ce rarar kudaden da Ofishin Kasafin Kudi ya ce an tara a shekarar 2017 da 2018 sun zarce tantagaryar adadin kudaden da ita hukumar ta NPA ta tara.

“Saboda Kididdigar Bin-diddigin da aka yi wa Asusun NPA a shekarun 2027 da 2018 sun tabbatar da an samu rarar naira biliyan 76.782 da naira biliyan 72.480 a shekarar 2017 da 2018.

Hadiza ta ce “zuki-ta-malle ce da masu bincike daga Ofishin Kasafin Kudi su ka ce NPA ta samu rarar naira biliyan 133.084 da naira biliyan 88.79 a shekarun 2017 da 2018.”

Ta kara da cewa, “manhajar da Hukumar Tabbatar da Tara Kudade ta shimfida sun tsaya a kan gejin naira biliyan 52.09 a shekarar 2027, sai kuma naira biliyan 42.51 a shekarar 2018. Kuma mu ka tara wa Gwamnatin Tarayya kashi 80% bisa 100% na kudaden, kamar yadda doka ta tanadar, wato naira biliyan 40.873 a 2017 sai naira biliyan 34.065 a 2018.

Batun kudaden 2019 da na 2020, Hadiza ta ce NPA na jiran amincewar kididdigar Hukumar Gudanarwar NPA wadda za ta rattaba adadin abin da za a zuba a asusun Gwamnatin Tarayya.

Amma duk da haka, ta ce NPA ta zuba naira biliyan 31.683 a 2019, sai kuma naira biliyan 51.049 a 2020.

Masu Hada-hadar Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Goyi Bayan Dakatar Da Hadiza:

Wasu masu ruwa da tsaki a hada-hadar harkokin tashoshin jiragen ruwa a Lagos sun goyi bayan dakatar da Shugabar Hukumar NPA, Hadiza Bala Usman domin a yi bincike.

Sun bayyana cewa ai ba wani abu ba ne don wanda ya dauke ka aiki ya ce zai bincike ka, idan har ya fahimci ta kasa tabuka abin da aka nada ka don ka yi.

Shugaban Cibiyar Hada-hadar Jiragen Ruwa ta Najeriya (NIS), Kaftin Tony Onoharigho, ya ce dakatar da Hadiza ba laifi ba ne idan har ta aikata laifin dakatar da ita din.

“Amma dai a yanzu ba a san laifin da ta yi din ba tukunna. Idan ta yi laifi, to an yi daidai.

“Dama ai Gwamnatin Tarayya ce ta nada ta, to idan gwamnatin ta ga ba ta tabuka abin kirki, a cire ta kawai.

“Amma idan ba ta aikata laifin komai ba, mu ka fahimci bi-ta-da-kulli ake yi mata, to za mu daura banten kokawa da gwamnatin tarayya.”

Onoharigho ya ce shi shawarar sa ma bai kamata a rika nada wani shugabancin NPA har a bar shi ya dade sosai a wurin ba.

Ya ce a rika sauya wa NPA shugaba bayan ‘yan shekaru kalilan, domin a bai wa wani gogagge kuma kwararren da shi ma zai hau ya bayar da ta sa gudummawar.

Share.

game da Author