Kwamitin Lura da Harkokin Mai na Majalisar Tarayya ya gargadi Shugabannin NNPC su bayyana a gaban sa cikin kwanaki 14, domin a samu damar warware wani cukurkudadden kulli.
Da ya ke bayanin gargadin, Shugaban Kwamitin Lura Da Harkokin Mai, Sarki Adar, dan APC daga Jihar Sokoto, ya ce idan wa’adin kwanaki 14 su ka cika NNPC ba su bayyana a gaban sa ba, to babu makawa za su gayyaci Shugaba Muhammadu Buhari domin shi ne Ministan Man Fetur na Kasa.
Wannan batu ya taso ne sakamakon wata dambarwar soke lasisin hakar man fetur da kuma soke sokewar farkon da aka yi ta lasisin hakar rijiyoyi masu lamba OML 123, 124, 126 da kuma 137.
Wadannan kadarorin danyen mai sun kasance abin dambarwa tsakanin wasu kamfanoni mallakar ‘yan Chana da kuma Gwamnatin Tarayya.
Takun-saka a tsakanin su ya haifar da soke lasisin da kuma mayar da lasisin, wanda Gwamnatin Buhari ta yi.
A ranar Alhamis dai NNPC, Addax Petroleum Explorarion Nigeria Ltd, Kaztech Engineering Ltd da Salvic Petroleum Resources Ltd duk sun kasa bayyana a gaban kwamitin majalisar.
Amma kuma Karamin Ministan Fetur, Timipriye Slva da Shugaban Bangaren DPR, Sarki Auwalu duk sun bayyana a gaban kwamitin.
Yayin da NNPC ta mi bayyana, amma ta aika wa wasika cewa rigimar ta kotu, shi kuma Karamin Ministan Fetur, Sylva, cewa ya yi maganar ba ta gaban Kotun Koli kamar yadda NNPC ta bayyana cikin wasikar da ta aika wa kwamiti.
“Tunda NNPC ta ki bayyana, za mu abin da ya dace a mataki na gaba, wato mu gayyato Shugaba Buhari a matsayin sa na Ministan Man Fetur.
“Ina mika wannan sanarwa ga dukkan bangarorin da su ka ki bayyana a gaban kwamiti da su bayyana nan da kwanaki 14.
“Idan su ka ki kuwa za mu gayyato Ministan Fetur, wato Shugaba Buhari. Na san tunda mutum ne mai biyayya ga dokar kasa, bayayya ga doka, bayyana zai yi. Daga nan sai mu sanar da shi cewa NNPC ta yi watsi da gayyatar da aka yi masa.
Idan ba a manta ba, DPR ta soke lasisin kamfanin Addax, wanda a yanzu wasu ‘yan Chana ne su ka mallaki lasisin a karkashin wani kamfani mai suna Sinopec.
Wani kwamitin da shugaban kasa ya kafa ne a karkashin shugabancin tsohon Sanata, Magnus Abe ya zargi kamfanin na mai da ‘janyo wa tattalin arkizi asara.”
DPR ta soke kwangilar saboda wadannan kamfanonin hakar mai, OMLd sun kasa kiyayawa da sharuddan da aka gindaya masu.
Bayan an soke na su lasisin, sai aka bai wa wasu kamfanonin cikin gida, wato Kaztec Engineering Limited/Salvic Petroleum Resources Limited.
Bayan nan kuma, ko makonni biyu ba su cika ba, sai Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar da sanarwar cewa an maida lasisin na Rijiyoyi masu Lasisin OMLs 123, 124, 126 da 137 ga NNPC, wadda ke da yarjejeniyar hadin-guiwar hako danyen mai tare ds Addax Petroleum.
Wato kenan an sake maida lasisin ga Addax.
Sai dai Karamin Minista Sylva ya ce NNPC ta yi azarbabin rubuta ba’asin ta ga Addax, kafin shi ya amince.
“Na rubuta wa Shugaban Kasa wasika, kuma ya amince. Ita kuma NNPC ta rubuta wa Shugaban Kasa wata takardar da ta saba wa tawa.
“Don haka maida lasisin ga Addax bai karya wata doka ko daya ba. Kuma ni dai ban san akwai wannan dambarwar a gaban Kotun Koli ba.” Inji Sylva.
Discussion about this post