Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa saura kiris dakakrun Najeriya su hallaka ‘yan bindigan da suka sace daliban Afaka da ruwan bama-bamai kafin Allah ya ceto su.
El-Rufai ya bayyana haka ne a jawabin da yayi a taron ‘African Leadership Group’.
” Dole za a rasa wasu dalibai amma kuma hakan ya fi mana maimakon mu biya ‘yan bindiga kudin fansa. Idan aka yi musu ambaliyar bama-bamai za a kashe dukan su, kuma za a ceto wasu dalibai da rai, hakan yafi maimakon mu biyan kudin fansa.
” Mun san tabbas akwai hadari a yin haka, amma kuma muka yarda hakan za a yi saboda a irin wannan yaki dole a rasa wasu muddun ana so a yi nasara akai.
El-Rufai ya nanata a lokutta da dama cewa shi ko gwamnatin sa ba za su biya kudin fansa akan kowani mutum da ‘yan bindiga suka sace ba. Ya ce ko da ko dansa aka sace, sai dai su yi sallama da shi, sannan yayi masa fatan Allah ya hada su a Aljannah, amma ba zai biya su ko sisi ba.
Mahara sun saki ‘yan makarantar gandun Daji 27 dake tsare da su a daji kwanaki 55 bayan suna tare da su.
Tuni dai har an hada daliban da iyayen su ranar Juma’a.