Ministan Sadarwa Isah Ali Pantami ya bayyana cewa wasu kalaman da yayi a baya, dalili ne yasa yayi su a wancan lokaci wanda a yanzu ba haka suke ba dole karatunsa da ra’ayinsa akai su canja.
Pantami ya fadi haka a wajen tafsiri da yake yi a masallacin Annor, dake Abuja.
Pantami ya ce ya fara yin wa’azi tun yana shekara 13. Akwai abubuwan da ya fadi wanda a wancan lokaci bai yi nadamar su ba domin abinda ya sani kenan game da hakan a wancan lokaci amma kuma da karatu yayi karatu a’amura suka canja shima dole ya karkata zuwa ga yadda suke a yanzu.
” Amma da al’amura suka canja, dole wadannan matsaya nawa a wancan lokaci su canja yanzu. Saboda haka ba lallai bane ace irin wadannan matsaya ne na kafe akai har yanzu dole su canja.”
Pantami yace ba laofi bane ace dalili ya sa wasu abubuwa sun canja, sabanin abinda ka yarda ko ka a baya sannan bayan sun canja kai ma ka canja na ka matsayar akai.
Na san dalilin da wasu dibgaggu ke danganta ni da ta’addanci – Minista Pantami
Ministan Sadarwa Isa Pantami ya nesanta kan sa daga dangantaka ko alaka kowace iri ce da ayyukan ta’addanci da ‘yan ta’adda.
A cikin wata tattaunawar musamman da ya yi da PREMIUM TIMES, Pantami ya bayyana cewa wasu rikakkun masu laifi da kuma masu wata boyayyar muguwar manufa ce ke kitsa masa wannan sharri.
Ya ce wasu gungun mutanen da ba su so ma’aikatar sa ta kididdige da sa-ido kan hada lambobin waya da katin dan kasa ne su ke ta kokarin tadiye kokarin da ya ke yi ganin ya tsaftace tsarin sadarwa, ya kakkabe salon shirya barna a zambar da ake yi a fannin sadarwa idan ba a yi wa lambobin waya da katin dan kasa rajista ba.
“Ko tantama ba na yi a kan haka. Sharrin da su ke kulla min na da nasaba da batun tilasta mallakar Katin Shaidar Dan Kasa da yi wa Layukan Waya Rajista hade da Lambar Katin Shaidar Dan Kasa.
“Shin ko ka san tun cikin 2011 aka fara bullo da batun hada layukan waya da katin shaidar dan kasa, amma abin bai yi nasara ba, saboda wasu gaggan batagarin boye su ka tadiye shirin.’ Inji Pantami.
Da aka tambaye shi sunayen wadanda su ka yi wa shirin tadiya bai yi nasara ba a 2011, sai Pantami ya kara da cewa, “Za ka iya shiga ka yi bincike a ‘online’ ka gani da idon ka a matsayin ka na dan jarida.
“Ko a cikin 2015 an bijiro da shirin nan, amma bai yi nasara ba, to sai cikin 2018 nan ma inda wasu lokuta aka yi taro tsakanin gwamnati da masu kamfanonin wayoyin selula na GSM. An mince cewa a karshen Janairu, 2018 za a tabbatar kowa ya hada rajistar layukan sa da lambar rajistar sa ta dan kasa. Amma hakan bai ywuwa, saboda wasu da ke da bakar aniyar kin amincewa a yi rajistar dan kasa tare da lamboyin waya su ka hana abin ya tabbata.
“Yanzu kuma sai su ka fara da watsa labaran karairayi wai jama’a daga kasashen da ke makwautaka da Najeriya na ta kwararowa su na yin rajistar dan kasa a cikin Najeriya. Amma kuma abin da su ka kasa ganewa shi ne ita lambar katin dan kasa NIN din nan fa ba ta dan Najeriya ba ce aka ce shi kadai za a yi wa. Duk wani mazaunin Najeriya zai iya yin wannan rajista, domin haka Sashe na 16 da 17 na Dokar Rajistar dan Kasa ta nuna.
“Dokar cewa ta yi da dan kasa, da mazaunin kasar nan bisa ka’ida, da masu iznin zama kasar nan tsawon shekaru biyu, duk za su iya yin wannan rajistar.
“Abin da kawai ake so shi ne ka gabatar da dukkan bayanan ka na lambar waya da adireshi da komai, ta yadda gwamnati a ta iya sanin duk wani motsi da ke yi ta hanyar gane bayanan ko kai wane ne a cikin kankanen lokaci.
“Kuma wadannan bayanai babu mai iya shigar su daga waje, sun zama na Hukumar NICM kadai. Wanda ya kutsa ya saci bayanan zai fusktanci tuhumar daurin shekaru goma.
“To wannan aikin ne mutanen boyen da ke aikata mayan laifuka ba su so, domin duk motsin aikata wani laifi da za su yi za a iya ganewa. Kuma a cikin sauki za a kama mutum. Aiki ne gagarimi na dakile laifuka, shi ne mutanen da ba su so shirin ya yi nasara ke ta kokarin shirya min sharrin alakanta ni da ta’addanci.”
Pantami ya ce duk wani sharii da za su kulla masa ba zai yi nasara ba, kuma ba zai sare masa guyawu ba.
‘Ka fahimta kuma ka lura cewa a matayin ka na ma’aikatacin gwamnati da ya kai wannan mukami, idan ka ce wasu za su yi maka wata barazana har su firgita ka, to ba za ka iya yin aikin ba kwata-kwata. Ko a ranar 12 Ga Afrilu ina tare da Jakadun Birtaniya, Amurka, Koriya ta Kudu da na wasu kasashe da dama.
“Duk wani babban mai laifi na cikin gida ko na waje ba zai so wannan aikin hada layukan waya da lambar katin dan kasa da mu ke yi ba. Saboda ya san ko ina ka aikata laifi za a iya gane ka a saukake.” Inji Pantami.